Hamas da Fatah sun cimma yarjejeniya kan Gaza | Labarai | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas da Fatah sun cimma yarjejeniya kan Gaza

Kungiyoyin Fatah da Hamas sun amince su mika ikon Gaza ga gwamnatin hadaka ta Faladinu.

Kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Hamas da Fatah sun cimma wata yarjejeniya a wannan Alhamis, inda gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagorancin Shugaba Mahmud Abbas za ta karbi iko da Zirin Gaza. Masu shiga tsakani a tattaunawar da bangarorin ke yi a birnin Alkahira na kasar Masar suka sanar da cimma wannan yarjejeniya. Azzam Ahmed na kungiyar Fatah ya ce dukkan ma'aikatan gwamnati za su rika samun albashi daga gwamnatin hadin kai domin dukkansu Falasdinawa ne kuma gwamnati ce ta dukkan Falasdinawa.