Hama Amadou ya tserewa rikicin siyasar Nijar | Siyasa | DW | 28.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hama Amadou ya tserewa rikicin siyasar Nijar

Yayin da rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar ke cigaba da zafafa, kakakin majalisar dokokin kasar ya tsere zuwa Burkina Faso baya da aka cire masa rigar kariya don fuskantar shari'a kan badakalar cinikin jarirai.

Kafofin yada labarai na radio da talabijin na gwamnatin Jamhuriyar Niger ne dai suka fara bada labarin tserewar ta Malam Hama Amadou daga cikin kasar zuwa Burkina Faso ko da dai ba su yi karin haske ba game da hakan. To sai dai a wata hira da ya yi da DW sakataren jam'iyyar ta Lumana Afrika Malam Maman Sani ya tabbatar da lamarin inda ya ce shugaban jamiyyar tasu ya dauki wannan mataki ne bisa shawarar uwar jam'iyyar tasa domin kaucewa barazanar kisa da ya ke fuskanta daga hannun gwamnati.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou

Gwamnatin Shugaba Mouhamadou Issufou ta musanta zargin da ake mata na matsawa 'yan adawa

Ficewar shugaban majalisar dokokin kasar ta Niger dai ta wakana ne 'yan awoyi kalilan bayan da kwamitin gudanarwar majalisar dokoki ya baiwa gwamnatin kasar izinin kama Malam Hama Amadou din domin mika shi a hannun kuliya don sauraransa a kan zarginsa da hannu a badakalar nan ta cinikin jarirai da ake zargin wasu 'yan Niger sun sayo daga Nigeria, to sai dai da ta ke tsokaci a kan wanann matakin gudun da shugaban jam'iyyar na Lumana Afrika ya dauka, jam'iyyar PNDS Tarayya mai milki ta bakin sakataran yada labaranta Malam Iro Sani cewa ta yi zargin da Hama Amadou din ya ke yi na kokarin kashe shi bai da tushe balle makama.

Har ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ta Niger ba ta kai ga cewa komi ba kan wannan lamari ba, yayin da a gefe guda al'ummar kasar ke zuba idanu don ganin irin tasirin da ficewar shugaban majalisar dokokin za ta yi ga tsarin aikin majalisar dama makomar siyasar shugaban majalisar da kansa da kuma gwagwarmayar da 'yan adawa ke yi da bangaran masu rinjaye a daidai lokacin da ya rage kasa da shekara daya da rabi Niger din ta yi zaben shugaban kasa.

Mawallafi: Gazali Abdou Tassawa
Edita: Ahmed Salisu/AH

Sauti da bidiyo akan labarin