Halin siyasar kasar Cote d´Voire | Labarai | DW | 21.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin siyasar kasar Cote d´Voire

A gobe ne Shugabannin kasashen Nigeria da Afrika ta Kudu da kuma Niger, zasu nufi kasar Ivory Coast domin taimakawa alúmar kasar wajen zabar sabo P/M a karkashin shirin wanzar da zaman lafiya. Wata sanarwa daga kasar Ivory Coast ta baiyana cewa shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo wanda kuma har ila yau shi ne shugaban kungiyar gamaiyar Afrika tare da shugaban kaar Afrika ta Kudu Thabo Mbeki dana Niger Tanja Mmadou kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS zasu isa kasar ta Cote d´Voire a gobe domin taimakawa alúmar kasar samun dawamammen zaman lafiya. Shugaban kasar Cote d´Voire Laurent Gbagbo ya sami sahalewar majalisar dinkin duniya ta karin waádin mulki na shekara guda ya zuwa lokacin da zaá gudanar da zabe a kasar a shekara mai zuwa. A makon da ya gabata ne yan adawar suka ýi fatali da jerin sunayen da aka gabatar na yan takara wadanda daga cikin su ne zaá zabi wanda zai zama P/M. A yanzu dai babbar matsalar dake fuskantar kasar ita ce ta zabar sabon P/M wanda zai sami amincewar dukkan bangarorin kasar.