Halin siyasa a Iraki | Labarai | DW | 11.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin siyasa a Iraki

Kawancen jam´iyun ´yan Shi´a a Iraqi wadda ta lashe zaben da aka gudanar cikin watan desamba ta dage shirinta har sai gobe lahadi na nada wanda zai rike mukamin FM. Majiyoyin jami´yun kawance sun ce bisa ga dukkan alamu mataimakin shugaban kasa Adel Abdul Mahdi wanda yayi makaranta a birnin Paris na Faransa, za´a nada a wannan mukami. To amma wasu kafofin kuma sun mayar da hankali akan Firimia Ibrahim al-Jafari. Kawance dai shi ya samu kujeru 128 daga cikin kujeru 275 na majalisar dokokin bayan an tabbatar da sakamakon zaben na cikin watan desamba, a jiya juma´a. Masu aiko da rahotannin sun ce nadin Mahdi zai ba da damar gaggauta kafa sabuwar gwamnati.