HALIN SIYASA A AFGANISTAN. | Siyasa | DW | 14.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN SIYASA A AFGANISTAN.

Yamutsi a Herat sakamakon tsige gwamna Ismail Khan.

Yamutsin Siyasa.

Yamutsin Siyasa.

Harkokin siyasa a kasar Afganistan dai na cigaba da daukan sabbin salo,ayayinda ya rage kasa da wata guda a gudanar da zaben shugaban kasa,a karo na farko tun bayan kifar da gwamnatin Taliban a shekara ta 2001.

Wata kungiyar kare hakkin biladama dake Afganistan ayau,tayi maraba da tsige gwamnan jihar Herat Ismail Khan daga mukaminsa,mutumin ake zargi da laifuffuka na take hakkin biladama a wannan gunduwa dake yammacin kasar.Kakakin hukumar Nader Ahmed Nadery,yace yin hakan da gwamnatin kasar tayi zai taimaka matuka gaya wajen inganta rayuwar jammaaa a Herat.Ana dai zargin tsohon gwamna Khan da laifin hanawa mata da kafofin yada labaru yancin tafi da ayyukansu,sai dai wasu ya zuwa yanzu na Alfahari da irin rawa daya taka a yaki da dakarun mamaye na Soviet daya gudana a shekarata 1979-89.

Tun bayan sanar da tubeshi ranar asabar data gabata birnin na herat ya kasance wani dandali na tashin hankali,musamman wa magoya bayansa.

A sakamakon hakane a ranar Lahadi sukayi zanga zangar da ta kaisu ga afkawa gine gine hukumomin Mdd dake garin da wasu hukumomi masu zaman kansu,harda sojin Amurka dana Afganistan din.Wannan yamutsi dai ya haddasa mutuwan mutane 4,banda masu yawan gaske da suka jikkata ciki harda sojin amurka 3.Bayan an kafa dokar hana yawo,tare da bayyana Khan a gidan talabijin inda yake kira ga magoya bayansa dasuyi hakuri ne,aka samu lafawan lamura a jihar ta Herat.

A hamnnu guda kuma jamian agaji na kasa da kasa dake aiki a garin na Herat sun bayyana takaicinsu dangane da rikicin siyasar gunduwar daya ritsa dasu,wanda a haddasa yawancin maaikatansu tserawa da rayukansu.Sakamakon wannan yamutsin dai an rusa tare da kone ofisoshinsu da dama, batu daya sanya MDD ta janye maaikatanta kimanin 60 daga Herat,a jiya Litinin.

Magoya bayan tsohon gwamna Khan dai sunyi wannan zanga zanga ne da nufin bayyana bacin ransu da matakin da Shugaba Hamid Kharzai ya dauka da gwamnatinsa wajen kora ,tare da maye gurbin gwamnansu,abunda ake zargi da matakan neman nasaran shugaban,a zaben dazai gudana a watan Oktoba a wannan gunduwa,dake yammacin Afganistan.

Kakakin MDD a Afganistan,Manoel Silva,ya bayyana yamutsin Herat din da kasancewa mafi munin irinsa wa hukumomin agaji na kasa da kasa ,tun bayan kifar da gwamnatin yan Taliban.

To sai dai Sabon gwamnan Herat Sayed Mohammad Khairkhwa,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa,yayi fatan jamian agajin da suka janye daga gunduwar sakamakon wannan rikici zasu komo domin cigaba da aikinsu.Yace ya gana da jamian MDD wadanda suka koka da abunda ya faru,kuma yayi musu alkawrin cewa abu makamancin haka bazai sake faruwa ba.Ya kara dacewa hakki ya rataya a wuyansu na tabbatar da kariya wa jamian agajin da gine ginensu.

Shi dai Khan na mai zama daya daga cikin shugabannin haulolin Afganistan,kuma dan kabilar Tajik,wanda har yanzu ke zama gwarzon namiji a Afganistan,mutumin da kuma ya takarawar gani wajen yakin kifar da gwamnatin Yan Taliban a karshen ashekarata 2001.Duk dacewa ya samu mulki bayan kifar dasu,hakan bai hanashi cigaba da yakan sauran shugabannin hauloli dake makwabtaka dashi ba.Sabon Gwamna Sayed yace an bashi wannan mukami ne domin ya samar da zaman lafiya a wannan gunduwa.

Zainab A Mohammed.