Halin rashin sanin tabbas a gabacin Kongo | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Halin rashin sanin tabbas a gabacin Kongo

Fararen hula suka fi jin jiki a rikicin gabacin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, wanda ba a hango hanyar warware shi ba.

A wannan makon ma jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan halin da ake ciki a gabacin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo. A labarin ta jaridar Neues Deutschland ta fara ne da cewa.

„Har yanzu ana cikin halin rashin sanin tabbas a gabacin Kongo. Duk da ƙoƙarin shiga tsakani da ƙasar Uganda ta yi, 'yan tawayen ƙungiyar M23 sun amince su janye daga garin Goma bisa wasu sharuɗɗa. Jaridar ta ce fararen hula suka fi jin jiki a wannan rikicin da ba a hango hanyar warware shi a siyasance ba. Ƙwace garin na Goma na zaman wata dama ga 'yan tawayen ta tilasta wa gwamnatin Kongo ta shiga tattaunawa da su kai tsaye, ko da yake an fara shawarwarin da su a bayan fage. Ga ƙasashen duniya dai abubuwa biyu ne ke da muhimmanci, na farko mawuyacin halin da jama'a ke ciki, na biyu aikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Kongo wato Monusco wadda ta gaza. Majalisar Ɗinkin Duniya ka iya amfani da abubuwan dake faruwa yanzu domin sake nazarin ayyukanta na siyasa. Wani abin da ya kamata a yi shi ne a mayar da hankali wajen kare fararen hula.“

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci a kan rikicin na Kongo ta na mai cewa ana cikin ruɗani a Goma, mako guda bayan 'yan tawaye sun ƙwace garin.

„Mazauna garin Goma ba sa hangen wata makoma kyakkyawa in ban da hali na rashin sanin tabbas. A hanyar dake tsakanin Goma da Sake mai tazarar kilomita 30 yamma da Goma, mutane a tagayyare ke kai komo, inda da yawa daga cikinsu ke komawa gida. Jaridar ta ce irin ruɗani da mutanen ke ciki na nuni da taɓarɓarewar al'amura mako guda bayan 'yan tawayen M23 sun ƙwace iko a babban birnin lardin Kivu ta arewa.“

Rundunar Cote d'Ivoire barazana ga Ouattara

Daga rikicin 'yan tawaye a gabacin Kongo sai na siyasa a ƙasar Cote d'Ivoire. A labarin da ta buga mai taken "Doguwar hanyar cimma zaman lafiya a ƙasar Cote d'Ivoire, jaridar Neues Deutschland cewa ta yi:

Alassane Ouattara Präsident

Alassane Ouattara

„Shekaru biyu kenan da Alassane Ouattara ya ka da Laurent Gbagbo a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu, abin da ya ƙaddamar da sauyin mulki a Cote d'Ivoire. A wancan lokaci ƙasar ta tsunduma cikin wani yaƙin basasa na tsawon watanni. An kawo ƙarshen wannan rikici amma har yanzu matsalolin da suka haddasa su, suna nan. Jaridar ta rawaito wani rahoto da ƙungiyar ƙasa da ƙasa dake bin diddigin tashe tashen hankula wato International Crisis Group-ICG- ta bayar a kan halin da ake ciki a Cote d'Ivoire da cewa ba abin farin ciki ba ne ga shugaba Alassane Ouattara. Kwanaki biyu kafin zagayowar shekaru biyu da nasarar zaɓen na ranar 28 ga watan Nuwamban shekarar 2010, ƙungiyar ICG ta wallafa rahoton mai taken rage hauhawar tsamari a Cote d'Ivoire. Ƙungiyar ta yi nuni da cewa shugaba Ouattara ka iya fuskantar babbar barazana ta dagulewar lamura daga sojojinsa, saboda mummunar ɓaraka dake tsakanin rundunar ƙasar da ta ƙunshi masu biyayya ga tsohon shugaba Gbagbo da kuma tsoffin 'yan tawaye masu bin aƙidoji dabam dabam.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman