Halin da ′yan adawa ke ciki a Kongo | Labarai | DW | 19.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da 'yan adawa ke ciki a Kongo

Wata kotu a birnin Kinshasa ta tuhumi jagoran adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, wanda kuma ya tsaya takarar shugabancin kasar Moise Katumbi da aikata laifin cin amanar kasa.

Babban lauyan gwamnatin kasar ne dai ya bayyana wannan tuhuma a wani zama da kotun ta yi a wannan Alhamis, wanda ke zaman mataki na karshe na sauraren karar da gwamnatin ta shigar kan dan adawar kafin soma zaman shari'ar na gadan-gadan kan batun nasa. Idan dai har kotun ta same shi da aikata wannan laifi na zargin cin amanar kasa, to kuwa tana iya yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na daurin rai da rai .

A hannu guda kuma gwamnatin kasar ta bada sammacin kamo Moise Katumbi a bisa zargin daukar sojojin haya a jihar Katanga inda ya rike mukamin gwamna daga shekara ta 2007 zuwa ta 2015. Wasu na kusa da Moise Katumbin dai sun ce a halin yanzu Katumb na akwance a wani asibiti na birnin Lubumbashi da ke Kudu maso Gabashin kasar.