Halin da Kony na ƙungiyar LRA ke ciki | Labarai | DW | 20.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da Kony na ƙungiyar LRA ke ciki

shugaban ƙungiyar tawaye ta LRA Joseh Kony da ake nema ruwa a Jallo ya na Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, amma kuma ba shi da lafiya, in ji shugaban ƙasar Michel Djotodia .

A picture taken on November 12, 2006 of then leader of the Lord's Resistance Army (LRA) Joseph Kony answering journalists' questions at Ri-Kwamba, in Southern Sudan. A former child soldier at the heart of a viral campaign to bring accused Ugandan war criminal Joseph Kony to justice said on March 9, 2012 he backed the video and urged people to watch it. It's a hard movie, Jacob Acaye told ABC News about the 30-minute video that has garnered nearly 58 million viewers since Monday. AFP PHOTO/ POOL - STUART PRICE (Photo credit should read STUART PRICE/AFP/Getty Images)

Joseph Kony

Bisa ga dukkanin alamu shugaban ƙungiyar tawaye ta LRA da ake nema ruwa a jallo wato Joseph Kony ya na fake yanzu haka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Shugaban riƙon ƙwarya na wannan ƙasa Michel Djotidia ne ya tsegunta ma wani babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Bangui wannan labari. A cewarsa dai Kony da ke fama da rashin lafiya yanzu haka ya tattauna da shi inda ya nemi mafaka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Kotun hukunta manyan laifukan yaƙi da ke da mazauninta a birnin The Hague ta ne neman cafke Joseph Kony ɗan asalin Yuganda da kuma wasu muƙarrabansa uku, bisa zarginsu da ta ke yi da aikata laifukan yaƙi. Ita ma dai ƙasar Amirka ta yi alƙawarin bayar da lada mai tsoka ga duk mutumin da ya taimaka a kama jagoran kungiyar LRA.

Wani rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya nunar da cewa mutane dubu 100 wannan ƙungiyar ta LRA ta kashe a ƙasashen yankin tsakiyar Afirka a cikin shekaru 25 da suka gabata. Hakazalika ta sace darurruwan yara ne LRA ta sace, yayin da mutane miliyan biyu da dubu 500 suka ƙaurace wa matsaugusu sakamakon tashin hankali da ta ke haddasawa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahamane Hassane