Halin da gwamnatin hadakar kasar Nijar ke ciki | Siyasa | DW | 18.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Halin da gwamnatin hadakar kasar Nijar ke ciki

Shekara guda bayan kafa gwamnatin hadaka ta Jamhuriyar Nijar ana ci gaba da samun cece-kuce dangane da fannonin siyasa da na tattalin arziki da kuma na zamantakewa.

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou

Shugaba Mahamadou Issoufou (a dama) da Hama Amadou Shugaban majalisar dokoki (a hagu)

Shekara guda bayan da Shugaba Issoufou Mahamadou na Nijar ya kira 'yan siyasa da su kama domin kafa gwamnatin hadaka, matakin da a can baya ya haifar da rudani tsakanin 'yan kasar. Shin ana iya cewa hakarsa ta cimma ruwa?

Rikicin siyasar jamhuriyar ta Nijar na baya-bayan nan ya dauko asali ne tun bayan da Shugaba Issoufou Mahamadou ya bukaci a dama da su a cikin al'amuran tafiyar da kasar a watan Augustan shekarar bara ta 2013. Shekara guda bayan tayin ina aka kwana?

Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger

Hama Amadou a tsakiya yayin zaman majalisar dokoki

Camarade Moumouni Habibhou mamba a hadin gwiwar jerin kungiyoyin fararen hula na CDTN cewa ya yi akwai nasara amma wasu 'yan siyasa sun nemi wargaza shirin.

To saidai Camarade Abdoulaziz Bouboucar daga hadin gwiwar CEPRASE ta malaman koyarwa ya ce babu wani hadin kan da aka samu.

Babu shakka an samu nasara ga matakin da Shugaba Issoufou Mahamadou ya dauka shi ne na tarwatsa jam'iyoyin siyasa na adawa domin cimma wani buri inji Alhaji Abdoulmoumouni Duluhu kakakin hadin gwiwar jam'iyoyin adawa na AMRN.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012

Brigi Rafini Firaministan Jamhuriyar Nijar

A lokacin da yake mayar da martani, Malam Assouman Adamou mai inkiyar Mani, da ke magana da yawun jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki, ya zargi jam'iyyun na adawa da yunkurin yi wa gwamnati kafar angulu.

Wannan lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar ci-gaban al'umma ta kasa da kasa UNDP ko PNUD ta ba da rahoton cewa daga Jamhuriyar Nijar sai kurar mota bisa ci-gaban al'umma.

Mawallafi: Issoufou Mamane (daga Tahoua)
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin