.: HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 18.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

.: HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

SHUGABA BUSH DA SILVIO BALUSCONI DAYA DAGA CIKIN MUTANEN DA SUKA RUFAWA BUSH BAYA AKA KADDAMAR DA YAKI A IRAQI.

default

Ministan tsaro na kasar Iraqi Hazem Al shalan yace za a fara wani binciken kwakwaf na laluben mutanen da ake zargi nada hannu a cikin harin nan na kunar bakin wake da aka kai a safiyar jiya Alhamis,wanda sakamakon hakan mutane 35 suka rasa rayukan su wasu kuma 145 suka jikkata.

Ministan ya tabbatar da cewa binciken zai wakana ne gida izuwa gida sako izuwa sako da kuma lungu izuwa lungu don nemo wadan da keda da hannu a cikin tashin bama baman biyu.

Mr Hazem Al shalan ya kara da cewa idan ta kama a yankewa wadanda aka samu da laifi kann hakan to babu makawa za a aiwatar da hakan don hakan ya zama darasi ga yan baya.

Shi kuwa ministan cikin gida na iraqi Al Naqib cewa yayi wan nan harin kunar bakin wake babu shakka nada nasaba da dan taaddar nan na kasar Jordan wato Abu Musab Al Zarqawi.Ministan cikin gidan na iraqi ya kuma zargi wasu yan kasashen ketare dasa hannu a cikin wan nan harin na kunar bakin wake,to amma kuma ya gaza bada cikakkun bayanai dake tabbatar da hakan.

A yayin da ake cikin wan nan hali a daya hannun kuma an fuskanci wata arangama a tsakanin yan fadan sari ka noken da kuma dakarun sojin hadin giwar a Garin Buhriz wanda ke arewa maso gabashin birnin Baqouba.

A cewar Major Janaral Neal yan fadan sari ka noken sun kai musu hari ne a sansanin da suke a wan nan yanki bisa hakan ne kuwa a cewar su jamian sa suka mayar da wuta wanda hakan yayi sular mutuwar mutum biyu daga cikin yan fadan sari ka noken.

Wan nan dai gari na Baqouba yayi kaurin suna wajen fuskantar tashe tashen hankula a tsakanin bangarorin biyu,musanmamma ganin cewa a nan ne yan darikar Sunni dake marawa Saddam Hussain baya suka fi yawa.

A wata sabuwa kuma a yau juma a ne gwamnatin kasar Japan ta zartar da kudurin kyale dakarun su dake iraqi ci gaba da zama a kasar bayan mika mulki hannun yan kasar a karashen wan nan da muke ciki.

A can baya dai dakarun kasar na Japan na gudanar da aikin bayar da agajin gaggawa ne a maimakon tabbatar da tsaro da kuma dunkiyoyin alummar kasar.

Haka itama kasar Koriya ta kudu ta amince da aikewa da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya dubu uku izuwa kasar ta iraqi. Za dai a fara aikewa da dakaru 900 daga watan Agusta na wan nan shekara da muke ciki izuwa garin Erbil don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya.

A daya hannun kuma mataimakin sakataren tsaro na Amurka Paul Wolfowitz ya tabbatar da cewa kasar sa a shirye take ta bawa gwamnatin wucin gadi ta iraqi duk wani goyon baya da ake bukata wajen ganin mulkin dimokradiyya ya inganta a wan nan kasa yadda ya kamata bayan mika mulki hannun yan kasar.

A daya ban garen kuma shugaba Bush na Amurka har yanzu yace yana nan akan bakansa na cewa harin nan da aka kaiwa Amurka na sha daya ga watan satumba nada alaqa da Saddam Hussain ko kuma kasar iraqi.

Shugaban na Amurka ya jaddada matakin sa da cewa Saddam Hussain nada nasaba babba da kungiyoyin yan taadda na Alqeeda.

A dai jiya alhamis ne rahoton bincikemn musabbabin kawowa Amurká harin na Sha daya ga wata ya musanta wan nan zargi na fadar ta White House da cewa babu kanshin gaskiya a cikin sa.

IBRAHIM SANI.