1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Angola

January 9, 2010

Angola na fama da rashin nagartattun hanyoyin sadarwa na zamani

https://p.dw.com/p/LPQ4
Buɗe bikin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin ƙasashen Afirka a AngolaHoto: AP

A wannan makon ne ake fara gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin ƙasashen Afirka a ƙasar Angola. Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi amfani da wannan dama domin duba halin da ake ciki a ƙasar. Jaridar ta ce:

"Ƙasar Angola, mai karɓar baƙoncin wasannin ƙwallon ƙafa na cin kofin ƙasashen Afirka, a shekarar ƙwallon ƙafa ta Afirka, har yau tana fama da tasirin yaƙin basasar da ta sha fama da shi har ya zuwa shekara ta 2002. Ƙasar na fama da ƙarancin nagartattun hanyoyin sadarwa na zamani ta yadda babban birninta Luanda a idanun Turawa ya zama shi ne mafi tsadar rayuwa a tsakanin birane na duniya. Wannan ma dai shi ne dalilin da ya sanya 'yan jarida da masu yawon buɗe ido da dama ba zasu iya shaidar da wasannin na cin kofin ƙasashen Afirka na bana ba."

Ƙasar Guinea na ci gaba da ƙoƙrin neman mafita daga cikin mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki, wannan shi ne take wani rahoto da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta ta kuma ci gaba da cewar:

Guinea Dezember 2009
Har yau ana fama da ƙaƙa-nika-yi da mulkin soja a ƙasar GuineaHoto: AP

"A halin da ake ciki yanzu haka ƙasar Guinea na fuskantar barazanar wargajewa kwata-kwata tun bayan mutuwar ɗan kama karya Lansana Konte a ranar 23 ga watan disemban shekara ta 2008, bayan mulki na tsawon shekaru 23. A ma dai wannan marra da muke ciki yanzu ba wani abin sha'awa game da mulkin ƙasar. Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Amirka da kuma Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ma ta haɗin kan tattalin arziƙin Afirka duk sun ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi. Abu mafi alheri dai a yanzu shi ne ƙasashen yammacin Afirka su tashi tsaye su shiga tsakani don sasanta rikicin tun kafin al'amuran ƙasar su zama gagara badau."

A sakamakon matsaloli na rashawa da cin hanci ana fuskantar matsalar sare dazuzzuka a tsuburin Madagaskar, kamar yadda jaridar Neues Deutsland ta rawaito ta kuma ƙara da cewa:

Brandrodung von Regenwald in Madagaskar Flash-galerie
Ɓannatar da kewayen ɗan-Adam a MadagaskarHoto: picture-alliance / OKAPIA

"A sakamakon gwagwarmayar kama madafun mulki ta aka sha fama da ita a tsuburin Madagaskar shekarar da ta wuce da kuma bala'in talaucin dake addabar al'uma, ana fama da wahala wajen kare muhalli da halittu a ƙasar. Matsalar tayi tsamari ne bayan maye gurbin shugaba Ravalomanana da aka yi, inda Andriy Rajoelina ya maye gurbinsa a shekarar da ta wuce, inda aka wayi gari ana sako-sako da manufofin kare kewayen ɗan-Adam, inda sannu a hankali ƙasar ke asarar yankuna masu ƙayatarwa da masu yawon buɗe ido ke sha'awar kai wa ziyara.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu