1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin ƙaƙakanikayi bayan girgizar ƙasa a China

April 15, 2010

Ma'aikatan ceto na ci-gaba da neman mutane a girgizar ƙasar da ta auku a China

https://p.dw.com/p/MwbT
Ma'aikatan ceto a ChinaHoto: AP

Ma'aikatan ceto a China na ci-gaba da haƙa a ƙarƙashin rusassun gine-gine, a ƙoƙarinsu na gano waɗanda suka tsira daga mummunar girgizar ƙasar da ta auku jiya a wani yanki dake arewa maso yammacin ƙasar, wadda kuma ta yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 600 sannan aƙalla 9000 suka samu raunuka. Dubban mutane sun kwana filin Allah Ta'ala a cikin wani yanayin sanyin hunturu. Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.9 a ma'aunin Richter ta aukawa wani yankin tsaunuka ne dake a lardin Qinghai, inda ta lalata kusan dukkan gidajen dake hedkwatar yankin. A halin da ake ciki ana fama da ƙarancin magunguna, tantuna, barguna da rigunan sanyi, kamar yadda wata mai ba da labarai a wata tashar telebijin ta nunar.

"Ma'aikatan ceto suna fama da ƙarancin kayan da ake buƙata, ba tantuna, ba rigunan sanyi, sannan da yawa daga cikinsu ba su da ruwan sha."

A halin da ake ciki Majalisar Ɗinkin Duniya da Amirka da kuma tarayyar Turai sun yi tayin ba da taimako.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu