Hakuri ya kai makura game da batun auren jinsi guda a Turai | Zamantakewa | DW | 04.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Hakuri ya kai makura game da batun auren jinsi guda a Turai

Matsalolin kudi a tarayyar Turai na kara karfafa bin tsohuwar al'ada ta zaman iyali amma a hannu daya suna adawa da canje canje a zamantakewa.

Yayin da ake wa kasar Faransa kirari na kasar da ke da kan gaba wajen yin daidaito tsakanin al'amuran da su ka shafi al'umma, a hannu guda masu auren jinsi daya na ganin wannan take ya saba da yadda kasar ta dauki masu auren jinsi wato 'yan madigo' da yan luwadi duk kuwa da cewa an kafa kungiyoyin fararen hula da ke kare muradunsu a cikin shekara ta 1999. Wannan na zuwa ne 'yan makonni kalilan kafin majalisar dattawan Faransan ta yanke hukunci kan sahale wa aure ga jinsi guda.

A daura da wannan turka-turka da ake, Cocin Katolika da 'yan jam'iyyun adawa masu ra'ayin rikau na cigaba da nuna adawarsu da kudurin dokar da 'yan jam'iyar Socilist ta kasar ta Faransa su ka mikawa majalisar dattawan kasar na amincewa da yin aure jinsi guda da ma basu sukunin yin rawar gaban hantsi kamar sauran al'umma to saidai masu kare muradun masu auren jinsi guda irin su Evelyne Paradis ta kungiyar ILGA-Europe na cewar matsayin da Cocin da ma wadanda ke rike da ra'ayin na mazan jiya a rude su ke sannan sun kasa sanya hankalinsu kan alkibla guda kazalika ransu a dugunzume ya ke.

"Sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da aka samu a duniya baki daya, ana kara samun yanayi na koma wa irin tsarin da ya ke a baya wato ra'ayi irin na mazan jiya."

People clash with riot police during a demonstration against France's gay marriage law in an attempt to block legislation that will allow homosexual couples to marry and adopt children, on March 24, 2013 in Paris. The hugely controversial bill to legalise same-sex marriage and adoption has been comfortably adopted by the lower chamber of parliament and will go to the Senate for examination and approval in April. AFP PHOTO / PIERRE ANDRIEU (Photo credit should read PIERRE ANDRIEU/AFP/Getty Images)

Arangama tsakanin masu bore da 'yan sandan Faransa

Baya ga wannan kalamai na uwargida Evelyne Paradis, a hannu guda kuma ta na ganin cewar zanga-zanga da ake a Faransa dangane da rashin amincewa da wannan batu na auren jinsi, 'yar manuniya ce ta kasar da za a iya cewa ba tsaro.

Kariya da 'yanci ga masu son bin salon rayuwa daban

A saboda wannan hali da aka shiga ne ya sanya Evelyne Paradis cewar a cikin shekaru goman da su ka gabata baya ga kariya da su bijiro da ita ta nuna wariya ga masu auren jinsi, sun kuma fidda wani tsari na bada kariya da kuma 'yanci alal misali na yin aure kamar kowa gami da daukar 'ya'ya ga wadanda ke da muradin badawa, batun da a halin yanzu ke zaman wani sauyi da aka samu saboda tunanin mutane ba su sauya cikin gaggawa ba idan aka yi la'akari da dokokin da aka shimfida kan wannan batu.

A halin da ake ciki, a mafi yawan kasashen da ke cikin kungiyar tarayyar Turai ba a amince da auren jinsi guda ba wato aure na 'yan luwadi da 'yan madigo. Kasashe bakwai ne kawai wadanda su ka hada da Denmark da Iceland da Spain ne su ka amince da auren na jinsi guda inda wasunsu ma ke amincewa da aure a coci yayin da wasu kasashen masu sassaucin ra'ayi su ka amince da zaman tarayya na masu neman jinsu guda kana kowacce kasa daga cikin kasashen 27 na kungiyar tarayyar Turai na iya zabar alkiblar da za ta dauka kan batun to sai dai wani batu da ke zaman kalubale ga masu neman jinsi guda ko ma yi aure shi ne bazun gado da na biyan haraji.

Abin kyama a wasu kasashe

Yayin da wasu kasashen na kungiyar tarayyar Turai ke goyon bayan auren jinsi guda, a hannu guda wasu kasashen musamman ma dai Italiya da Poland wanda ke bin darikar Katolika sau da kafa na da banbancin ra'ayi domin kuwa duk da kasancewarsu kasashen zaman tarayya ko kuma wajoko, ba su amince da irin wannan zama ba tsakanin masu neman jinsi guda.

Bildnummer: 59163784 Datum: 24.01.2013 Copyright: imago/Müller-Stauffenberg Jens Spahn (CDU, Gesundheitspolitischer Sprecher der CDU/CSU-Fraktion) in der Talk-Show maybrit illner am 24.01.2013 in Berlin Thema der Sendung: Hilfe, der Arzt kommt! - Wer stoppt den Medizin-Pfusch? People Politik Porträt x0x xsk 2013 quer 2012 Fernsehen Fernsehstudio TV Talkshow Show Talkgast Talkgäste ZDF Das Zweite maybrit illner Gast Gäste Diskussion Diskussionsrunde diskutieren Portrait Medizin Gesundheit Pfusch Behandlungsfehler Medizinopfer Behandlungsopfer Politiker Gesundheitspolitik Bundestagsabgeordneter CDU 59163784 Date 24 01 2013 Copyright Imago Mueller Stauffenberg Jens Spahn CDU health Spokesman the CDU CSU Group in the Talk Show Maybrit Illner at 24 01 2013 in Berlin Theme the Consignment Help the Doctor , Who Stop the Medicine Botch-up Celebrities politics Portrait x0x xSK 2013 horizontal 2012 Television Television TV Talk show Show Talk guest Talk guests ZDF the Second Maybrit Illner Guest Guests Discussion Round-table discussion discuss Portrait Medicine Health Botch-up Treatment errors Politicians Health policy Bundestag deputy CDU

Jens Spahn na jam'iyar CDU a Jamus

A bisa wannan ne ya sanya wasu ke ganin ya kyautu su ma masu neman jinsi guda su samu irin wannan 'yanci amma kuma a guji yin doka a kungiyar ta Tarayyar Turai game da hakan kamar yadda wasu ke son ganin anyi kamar dai yadda wani dan majalisa dokokin tarayyar Jamus na jam'iyyar CDU Jens Spahn ya shaida a wata hira da ya yi da gidan rediyon DW.

"In da Brussels za ta yadda da hakan to kila da ya zama doka to amma wannan ani abu ne da ba a amince da shi ba a tsakankanin al'umma ba."

To sai dai duk da wadannan kiraye-kirayen da ake da bayyana ra'ayoyi mabanbata, a hannu guda masu neman jinsi guda da wadanda ke kare muraduns na ganin muddin ba 'yanci aka basu ba to ya zama tamkar baya aka yi ba zani domin kuwa za su samu 'yanci a wasu kasashen yayin da wasu kasashen da ke kyamarsu ba za su ba su damar mike kafa ba.

Mawallafa: Sabrina Pabst / Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal