1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haiti na gudanar da zaben 'yan majalisa

Gazali Abdou tasawaAugust 9, 2015

'Yan takara 1855 za su fafata a neman kujeru 119 na 'yan majalisar dokoki da 20 na sanatoci. Mutane kimanin miliyon shida ne suka cancanci kada kuri'ar a wannan Karo.

https://p.dw.com/p/1GCMA
Wahlen Haiti Leslie Manigat
Hoto: AP

Rumfunan zabe kimanin 14000 ne dai hukumomin kasar suka tanada a cikin jihohi 10 na kasar a wannan zabe .Tun shekaru hudu da suka gabata ne dai ya kamata kasar ta Haiti ta shirya wannan zabe na 'yan majalisa, amma rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar ya hana gwamnati shugaba Michel Martelly samun damar shirya shi . Hakan ya sanya aka rusa majalisar dokokin kasar a farkon bana. Mutane kusan miliyan shida ne daga cikin sama da miliyan goma na yawan al'ummar kasar za su kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokoki 119 da sanatoci 20. 'Yan takara 1855 ne za su papata wajan neman kujerun 139.

Za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar da zagaye na biyu na 'yan majalissar dama na shugabannin kananan hukumomi a ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa.