Hadurran ababen hawa a duniya | Labarai | DW | 02.05.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadurran ababen hawa a duniya

WHO ta ce Matafiya a kasa dubu 270 ne ababen hawa ke janyo mutuwarsu a duk shekara.

Hukumar kula da harkokin Lafiya ta Duniya ta fitar da alkaluman mutanen da ke mutuwa sakamakon ababen hawan da ke kadesu a lokacin da suke tafiya a kasa, inda ta ce yawansu ya zarta dubu 270 - a duk shekara. A cewar Hukumar Lafiya ta Duniyar, matafiya a kasa da ke mutuwa su ne kaso 22 cikin 100 na adadin mutane miliyan daya da dubu 240 da ke mutuwa a kowace shekara sakamakon hadurran ababen hawa. Etienne Krug, da ke shugabantar sashen kula da matakan kariya ga jin rauni a hukumar lafiyar, ya ce kimanin matafiya a kasa dubu biyar ne ke mutuwa a kowane mako sakamakon ababen hawa da ke kade su. A bisa wannan dalilin ne ya bayyana bukatar daukar matakan bitar hanyoyin kariya ga lafiyar matafiya a kasa, tunda a cewarsa su ne matsalar yawan hadurran ababen hawa ta fi shafa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu