Hadin kan aikin raya kasa da kasashe masu fama da rikici
July 11, 2013Kasar Mali ta dauki lokaci mai tsawo tana zaman kyakyawar abar misali a tsakanin kasashen Afirka. Amma cikin lokaci kankane ta koma jerin kasashe masu fuskantar barazanar rugujewa. Tarayyar Jamus dake ba da taimakon raya kasa na fama da matsalolin yin hulda da irin wadannan kasashe kamar Mali dake yankin yammacin Afirka.
Yakin da aka shafe shekara daya da rabi ana yi a arewacin Mali da kuma dambarwar siyasa a Bamako babban birnin kasar sun bar babban tabo a kasar, inda aka tilasta wa dubbban daruruwan mutane barin yankunansu na asali. Tun gabanin yakin kasar ma Bankin Duniya ya nuna cewa fiye da rabin al'ummar kasar ta Mali na fama da matsanancin talauci da rashin ilimi da karancin tsabtataccen ruwan sha da kuma yawan mace-macen yara.
Mabanbantan matsaloli a kasashen da babu tabbas
Mali da kasashe kamar Somaliya, Cotre d'Ivoire da kuma Afghanistan na a jerin kasashe masu fuskantar barazanar rugujewa ko da yake matsalolinsu sun bambamta. Wibke Hansen ita ce mataimakiyar daraktan cibiyar nazarin ayyukan samar da zaman lafiya ta kasa da kasa dake birnin Berlin, ta yi karin haske a kan wanna batu tana mai cewa:
"Kasashe masu rauni ko suke da dab da rugujewa kasashe ne da ba sa iya tsaron yankunansu na cikin gida da kan iyakokinsu. Ba sa kuma iya tabbatar da ikon gwamnati da tsaron lafiya jama'arsu. Ba sa kuma da karfin samar da isasssun ababan more rayuwa kamar ilimi da kiwon lafiya ga al'umma."
Sama da rabin kasashen dake hulda da Jamus a bangaren hadin kan ayyukan raya kasa na a jerin kasashe dake fuskantar barazanar rugujewa ko kuma ke fama da rikice-rikice. Baya ga hadin kan ayyukan raya kasa wani muhimmin batu shi ne na tsaro, domin kasashen da ba sa iya tabbatar da tsaron kan iyakokinsu ko wasu yankuna na cikin gida, suna iya zama wata matattarar 'yan ta'adda.
Muhimmancin inganta lamirin tsaro
A bara ma'aikatar harkokin wajen Jamus da ta tsaro da kuma ta raya kasashe masu tasowa sun fitar da wani tsari dake nuni da yadda gwamnatin tarayyar Jamus za ta yi hulda da kasashe masu fama da rikice-rikice. Dirk Niebel shi ne ministan dake kula da hadin kan ayyukan raya kasashe masu tasowa na Jamus, da ya ce:
"Ba na jin gwamnatin Jamus za ta yarda wata kasa kamar Mali ta fada hannun kungiyoyin 'yan ta'adda. Yanzu haka baya ga sake gina kasar, muna kuma taimakawa wajen fadada tsare-tsarenta na tsaron kasa."
Sannu a hankali dai Jamus ta farfado da aikin taimakon raya kasa ga Mali bayan dakatar da shi a farkon shekarar 2012 biyo bayan juyin mulkin soji da sojoji suka yi a kasar. Burin aikin da Jamus din ke yi a Mali dai ya hada da sake daidaita al'amura a kasar wadda ke shirin gudanar da zabukan gama gari a ranar 28 ga watan Yuli.
Mawallafa: Sven Pöhle / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh