1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hada karfi a yunkurin shawo kan rikicin Mali

November 17, 2012

Kasashen Afirka ta ymama na kungiyar ECOWAS da Kungiyar Hadin Kan Turai sun daidaita game da bukatar hadin gwiwa kan matsalar yan tawaye a Mali

https://p.dw.com/p/16l0K
Hoto: picture-alliance/dpa

Jaridun na Jamus a wannan mako sun fi maida hankalinsu ne ga halin da ake ciki a Mali da kuma kokarin hada rundunar da zata kawar da mayakan kungiyoyin yan tawaye da suka mamaye arewacin kasar.

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba kokarin da kasashen Afirka ta yamma na kungiyar ECOWAS suke yi game da warware rikicin kasar ta Mali. Tace da farko wadannan kasashe sun yi kokarin warware matsalar ta hanyar tattaunawa, amma a yanzu sun yanke shawarar amfani da karfin makamai. Kungiyar ta ECOWAS a taron da tayi baya-bayan nan a Abuja, ta daidaita game da hada rundunar da zata kunshi sojoji 3300 da za'a tura arewacin kasar Mali, domin fatattakar mayakan yan tawaye, musamman na kungiyar Ansar Dine da suka mamaye yankin, kuma suke kokarin kafa yantacciyar kasar kansu. Jaridar Süddeutsche Zeitung tace wannan mataki na ECOWAS ya sami yabo daga mahukunta a Berlin, inda ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle yace ya kamata suma kasashen Turai suyi tunani cikin gaggawa game da kafa wata runduna, wadda akalla za'a danka mata alhakin horad da jami'an tsaron Mali yadda kasar zata iya kare kanta da kanta.

A game da irin gudummuwar da nahiyar Turai zata iya baiwa kokarin shawo kan rikicn yan tawaye a Mali, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhinta. Jaridar tace nahiyar Turai tana kan hanyar zuwa Mali, sai dai kuma rundunar tana iya fuskantar hadarori a aiyukan da zata yi. Kungiyar hadin kan Turai tana da niyyar bada sojoji tsakanin 200 zuwa 300 wadanda zasu hadu da takwarorin su na Aljeriya da Mauretaniya da na kungiyar ECOWAS domin horad da dakarun Mali. Rundunar ta hadin gwiwa za'a tsugunar da ita ne a Aljeriya.

Somalia neue Regierung Abdi Farah Shirdon Saaid Hassan Sheikh Mohamud
Shugabannin sabuwar gwamnatin SomaliyaHoto: Reuters

Jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan mako ta duba kisan gilla da aka yiwa yan sanda fiye da 30 a Kenya a wannan mako. Wannan hadari ya faru ne a lardin Samburu, inda wasu yan bindiga dadi a wani kauye suka aukawa yan sanda suka kashe 31 daga cikinsu. Yan bindiga dadin, inji jaridar, sun fito ne daga kauyen Turkana, kuma makiyaya ne a arewacin Kenya, bayan da aka tura yan sanda kauyen domin su kwato shanun da da yan kabilar Turkana din suka sace su daga abokan hamayyarsu, yan kabilar Samburu. Fashin shanu tsakanin yan kabilar Turkana da takwarorin su na Samburu ba sabon abu bane, an kuma sha samun dauki ba dadi da kashe kashe tsakaninsu. Makonni biyu da suka wuce rikicin da ya tashi a wnanan karo tsakaninsu ya kara tsananta, lokacin da yan kabilar Turkana suka kashe yan Samburu bakwai, suka kuma sace shanunsu kimanin 450.

A karshe, jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi a gamne da halin da yan jarida da manema labarai da wakilan kamfanonin yada labarai suke aiki karkashinsu a kasashen Afirka da dama. Jaridar tace a nahiyar Afirka, musamman a kasa kamar Somaliya, yan jarida suna rayuwar su ne cikin mummunan hali mai hadari. A kasashen Afirka da dama masu mulkin kama karya yan jarida dake kokarin gabatar da rahotanni na halin da shugabanni suke mulki, basu cika karewa lafiya ba. Duk dan jaridar da yayi kokarin tonawa da zurfi akan jefa shi gidan kaso, ko a azabtar dashi ko kisa. Abu mafi hadari musamman shine binciken shugabannin saboda dalilan cin hanci, ko cinikin makamai ko fataucin miyagn magunguna da cinikin haramun da albarkatun kasashen. To amma inji jaridar Süddeutsche Zeitung, babu inda dan jarida yafi rayuwarsa cikin hadari a Afrika fiye da a Somalia, inda kungiyar al-Shabaab take kan gaba wajen adawa da aiyukan yan jaridu da kafofin yada labarai.

Mwai Kibaki Präsident Kenia
Shugaban kasar Kenya Mwai KibakiHoto: dapd