1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Zaben majalisun dokoki a Habasha

Abdoulaye Mamane Amadou
June 21, 2021

Al'ummar Ethopia na ci gaba da kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki, wanda da ke zaman zakaran gwajin dafi ga Firaminista Aby Ahmed da ya yi alkawalin kawo sauyi a fagen siyasa.

https://p.dw.com/p/3vHo9
Äthiopien Wahl 2021 | Wahllokal Addis Abeba
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu komai na tafiya daidai game da zaban mai 'yan takara 9.500 daga jam'iyyun siyasa 40, duk da tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankin Tigrey tsakanin gwamnati da mayakan 'yan tawaye.

Sai dai masu adawa da gwamnatin Abiy, sun yi hannunka mai sanda, inda daya daga cikin ya bayyana cewa "Muna fatan zaben na wannan karon ba zai kasance tamkar irin wanda aka yi a can baya ba, ina mai cike da fatan ganin zaben ya kasance wanda zai assasa tubalin makomar wannan kasa da ka iya bai wa 'yan kasar wata sabuwar sa'ida."

Masu sharhi dai na ganin za a yi fafatawa mai tsanani a tsakanin bangarorin siyasar kasar da ke neman samun rinjaye don kafa gwamnati tare da kwace mulki a hannun firaministan da ya taba laashe kyautar duniya ta zaman lafiya.