Habasha ta fara sakin fursunonin siyasa | Labarai | DW | 17.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Habasha ta fara sakin fursunonin siyasa

Gwamnatin Habasha ta dauki matakin fara sakin daruruwan fursunonin siyasa da ke gidajen fursunoni na kasar inda babban dan adawa Merera Gudina yake cikin wadanda aka sako.

Gwamnatin Habasha ta dauki matakin fara sakin fursunonin siyasa inda tuni aka sako madugun 'yan adawa na kasar Merera Gudina wanda ya samu tarba daga dubban magoya baya. An saki wannan jigon 'yan adawan ne tare da wasu 'yan siyasa fiye da 100 daga gidan kurkukun da ke wajen birnin Addis Ababa. Kana an saki wasu 'yan furkuna 361 daga wurare daban-daban a yankin kudancin kasar ta Habasha kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.

Tuni jigon 'yan adawan Merera Gudina ya bukaci gwamnati ta yi tattaunawa ta hakika da 'yan adawa saboda shawo kan rikicin siyasa da ake samu a kasar ta Habasha da ke yankin gabashin Afirka.