Da me ake tuna Haile Selassie a Habasha?
September 12, 2024Sarki Haile Selassie wanda shi ne basarake na karshe da ya mulki Habasha, ya haye kan karagar mulki a shekara ta 1930, inda ya shafe tsawon shekaru 44 yana mulki kafin a tumbuke shi ta hanyar yi masa kisan gilla a ranar 12 ga watan Satumbar 1974. Tun da fari dai wata tawaga ce ta kwamitin sojoji da bai jima da kaddamar wa ba ta ziyarce shi a fadarsa da ke birnin Addis Ababa a daidai gabar karshe ta kawar da shi, bayan shafe tsawon watanni suna kitsa manakisar kifar da gwamnatinsa. Kuma cikin kalaman girmamawa, suka bukace shi da ya koma wani kebabben wuri don kare lafiyarsa. Ko da yake da farko ya nuna tirjiya, kafin daga bisani ya mika wuya. Bayan wasu jawabai da ya yi musu kan abin da ake nufi da shugabanci, sun yi awon gaba da shi a cikin mota.
Karin Bayani: Matsalar satar mutane na kara muni a kasar Habasha
Farfesa Hewan Semon Marye malama ce a jami'ar birnin Hamburg da ke nan Jamus, ta shaida wa DW cewa marigayi Sarki Haile Selassie gogarma ne sha kwaramniya. Kafin ya haye kan gadon sarauta, Sarki Selassie ya kasance cikin tawagar farko ta daliban da kasarsa ta aike zuwa Turai domin yin karatu bayan da aka nada shi a matsayin Yarima mai jiran gado a tsakanin shekarar 1916 zuwa 1930. Shi ne dai ya kaddamar da kundin tsarin mulkin kasar na farko a shekarar 1931, inda aka samar da majalisar dokoki da aka bai wa hurumin jeka-na-yi-ka wato dai ta bayar da shawara kawai, amma ba zartar da kudurin doka ba. A zamanin mulkinsa aka fara gina dam-dam na ruwa da tituna, sannan aka kafa rundunonin sojojin ruwa da na sama har ma da kamfanin sufurin jiragen sama na kasar.
Wani babban batu da 'yan kasar ke alfahari da shi idan har suka tuna marigayin shi ne, sadaukarwar da ya nuna domin tabbatar bunkasar ilimi da kuma ciyar da shi gaba. Daya daga cikin jikokinsa Asfa-Wossen Asserate ya tabbatarwa DW cewa, abin da za a rinka tunawa da shi da ya bari a baya shi ne bunkasa ilimi da har ma ake masa lakabi da baban ilimin Habasha bayan da ya kafa tubalin gina jami'a ta farko a kasar wadda ya tabbatar da wanzuwarta. Daga cikin manyan jagororin dunuya da suka kai masa ziyara Habasha, akwai Sarauniya Elizabeth ta biyu ta Burtaniya da Marshal Tito na Yugoslavia. Ya kuma samu zarafin yin tozali da Mao Zedong na Chaina a birnin Beijing da wasu shugabannin Amurka, ciki har da Richard Nixon da Dwight Eisenhower da Franklin Rooservelt da kuma John F. Kennedy.
Karin Bayani: Habasha za ta amince da 'yancin Somaliland
Ziyararsa ta farko zuwa Jamus, ya yi ta ne a shekarar 1954. Jamus din ta kasance babbar abokiyar dasawarsa, kuma alaka ta ci gaba da yaukaka tsakanin Habasha da Jamus har bayan mutuwarsa. Ko da yake ya yi fice wajen adawa da mulkin mallaka na kasashen yamma, kuma ya tsallake yaki da Italiya da nufin hambarar da shi. Ya taka gagarumar rawa wajen kafa kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka ta OAU a shekarar 1963, wadda a ake kira da Tarayyar Afirka AU. Mutuwar Sarki Haile Selassie ta janyo fadace-fadacen da suka haddasa zubar da jini har na tsawon shekaru 17, a tsakanin kabilun kasar ta Habasha.