1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin fara aiki da yarjejeniyar sulhu a Habasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 1, 2022

Gwamnatin Habashan ta sanar da cewa wani kwamitin hadin gwiwa na gwamnati da 'yan tawayen Tigray, na can a yankin na Tigraya a wani mataki na shirin karbar makamai daga 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/4KMU4
Habasha | Tigray | Rikici | Sulhu
Rikici ya halaka mutane da dama a Habasha, tare da tilasta wasu barin gidajensuHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Karbar makaman daga 'yan tawayen dai, na zaman wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka cimma a watan Nuwambar da ya gabata. Rikicin na Habasha da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana fama da shi, ya yi sanadiyyar asarar dimbin rayuka da dukiyoyi tare da tilasta dubbai kauracewa gidajensu.

Yarjejeniyar zaman lafiyar ta kunshi raba 'yan tawayen Tigray da makamansu cikin kwanaki 30, sai dai a nasu bangaren sun nunar da cewa hakan ba zai yiwu ba har sai bangaren gwamnati ya janye sojojin makwabciyar kasa Iritiriya da na yankin Amhara da ke makwabtaka da Tigray din da suka zo domin taya bangaren gwamnatin yaki.