1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada tsakanin gwamnati da 'yan TPLF

Binta Aliyu Zurmi
November 24, 2021

Gwamnatin Habasha ta bayyana cewar firaminista Abiy Ahmed ya tafi fagen daga domin jagorantar dakarunsa a yakin da suke yi da 'yan awaren yankin Tigray.

https://p.dw.com/p/43PvV
Äthiopien I Tigray-Krise
Hoto: AP/picture alliance

A lokacin da yake bayani a birnin Adis Ababa, Mai magana da yawun gwamnatin Habasha Legesse Tulu ya shaida wa manema labarai cewar tun a ranar Talata firaminista Ahmed ya danka wa mataimakinsa Demeke Mekonnen ragamar kasar domin zuwa fagen yaki. Sai dai ba'a bayyana takamaimai inda firaministan ya ke ba.

Shekara guda ke nan aka shafe ana gwabza fada a Habasha, kasa ta biyu mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Wannan rikicin dai ya yi sanadiyar rayukan daruruwan mutane gami da tilastawa wasu da dama barin matsugunansu.

Tuni kasashen yammacin duniya suka yi kira ga 'yan kasashensu da ke habasha da su gagauta barin kasar a daidai lokacin da fadan ke kara kazanta tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan awaren TPLF.