Haɗarin mota a Najeriya ya kashe mutane 36 | Labarai | DW | 06.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗarin mota a Najeriya ya kashe mutane 36

Haɗarin wanda ya auku a yankin kudu maso yammacin ƙasar, ya haddasa tashin gobara da ta ƙona gidaje da dama da ke kusa da inda lamarin ya faru.

default

Rahotanin daga yankin kudu maso yammancin Tarrayar Najeriya na cewar mutane 36 suka mutu a cikin wani haɗarin zirga zirga na mota wanda ya auku Kauyen Igbo-Gui da ke a cikin jihar Eddo.

Wanin kakakin 'yan sanda na jihar, Johanas Agwu ya shaidda cewar wata motar tanka ce dake dakon man fetir, ta ci karo da wata motar sapa ,abin da ya haddasa tashin gobarar da ta ƙone gidaje da dama dake a kusa da wurin da hatsarin ya auku. Wani shaidu wanda ya gane wa idanunsa, ya ce mutane uku kwai suka tsira da rayukansu a cikin motar ta sapa da ke ɗauke da fasinja da dama. Sannan kuma ya ce mai yiwuwa addadin mutane da lamarin ya rutsa da su, ya ƙaru saboda wutar gobarar da aka kwashe awowi ta na ci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi