Gyaran hali ga ′yan Boko Haram da suka mika wuya | Zamantakewa | DW | 11.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gyaran hali ga 'yan Boko Haram da suka mika wuya

Yayin da aka fara shirin sauya hali ga wasu mayakan Boko Haram 52 da suka tuba suka ajiye makamai, a karon farko an nuno wasu matakan da ake dauka na taimaka wa 'yan kungiyar da suka yi nadama.

Nigeria Boko Haram (DW/Al-Amin Suleiman Mohammad)

Wasu daga cikin tubabbun 'yan Boko Haram

Gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta kirkiro da wannan shirin domin bai wa mayakan Boko Haram da su ka zabi rungumar zaman lafiya ta hanyar sauya musu tunani da tsauraran akidun don zama 'yan kasa na gari tare da sake komawa cikin al'umma. Bisa wannan manufa ne rundunar sojin Najeriya ta kai wasu mayakan Boko Haram su 52 da suka ajiye makaman wani sansani da aka tanadar domin samun horon koyon sana'o'i daban daban. Ana sa ran shirin har ila yau, zai kyautata tunaninsu don zama masu bin dokoki kasa bayan tantance lafiyarsu ta jiki da kwakwalwa tare da gano hakikanin abin da ya shigar da su wannan kungiyar gami da yin adabo da mugunyar fafutukar.

Nigeria Boko Haram (DW/Al-Amin Suleiman Mohammad)

Tubabbun 'yan Boko Haram a dakunan kwanansu

Mai kula da wannan shirin, Manjo Janar Bamidele Shafa, ya ce za su basu kulawa da ta kamata kuma za a kiyaye musu hakkoki da kuma 'yanci yadda dokokin da yarjeniyoyin kasa da kasa suka tanadar. Manjo Janar Bamidele ya yi fatan shirin zai bada dama ga sauran mayakan kungiyar da ke ci gaba da gwagwarmaya don bin sahun wadannan da suka tuba a yanzu.

A karon farko rundunar Sojojin Najeriya ta bada dama ga wasu manema labarai su shiga wannan sansanin domin gane wa idanu yadda wajen ya ke musamman wuraren da za su sami horon na na sana'o'i da aka tsara.

Yayin da manema labarai su ka tambayi Manjo Janar Bamidele Shafa shugaban wannan shiri kan makomar tsofin mayakan Boko Haram din bayan kammala samun horo sai ya ce za a maida su cikin al'umomi ne, za kuma a sanya masu sa ido kan yadda su ke gudanar da rayuwa don tabbatar da cewa suna aiki da horon da aka basu da kuma bin dokokin kasa.