Gyaran fuska ga tsarin kuɗin EU | Labarai | DW | 15.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gyaran fuska ga tsarin kuɗin EU

Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) ta ɗau matakan yin garambawul ga tsarin hada-hadar kuɗinta

default

Takardun kuɗin Euro

Jami'an kula da harkar kuɗi a Ƙungiyar Tarayar Turai(EU) sun ɗau matakan kyautata tsarin tafiyar da kuɗin ƙungiyar. Komishinan kuɗin na EU, Michel Barnier ya ce matakan da suka ɗauka sun haɗa da inganta fannin kasuwanci. Ya bayyana cewa rashin tsarin lura da yadda ake tafiyar da kayayyakin da ake ƙerewa na masamman yana daga cikin abubuwan da ke ƙara dagular da halin da hada-hadar kuɗin duniya ta shiga. Matakan za su fara aikin nan da shekaru biyu, inda za su yi daidai da ƙa'idar da Amirka ta shimfiɗa na lura da bankuna da kuma kasuwannin hada-hadar kuɗi. A halin da ake ciki kuwa , cibiyar kuɗi ta ƙasa da ƙasa wanda ke wakiltan akasarin manyan bankuna a duniya, ta ce ana buƙatar Euro biliyan 545 a matsayin ajiya na jari ga kowane banki a sabon tsarin da aka yi, muddin dai ana son kauce wa shiga uku irin wanda  bankuna suka shiga sakamakon matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙin duniya . Waɗannan matakan suna da cikin tsarin da manyan ƙasashen duniya suka amince da su ƙarƙashin jagorancin Jamus da Faransa a wani mataki na riga kafi kan halin da duniya ta faɗa. Manyan bankuna ne dai za su fi a jika a wannan tsarin tun da sai su samar da kuɗin ajiya mai yawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas