1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara ga dokar dan asalin kasa ko yanki

January 28, 2014

'Ya'yan majalisun dokokin Najeriya na shirin yin gyara bisa dokar da ta banbanta dan kasa da ma bakinta da ake yi wa kallon ummul aba'isin tashe-tashen hankula a lokuta da dama.

https://p.dw.com/p/1Aydn
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A wani abun da ke zaman yunkurinta na kara dinke banbancin dake tsakanin sassan arewacin kasar da dan uwansa dake kudu , 'ya'yan majalisun kasar na shirin gyara bisa dokar da ta banbanta dan kasa da ma bakinta da ake yi wa kallon ummul aba'isin rigingimu a lokuta da dama.

A sassan kudancin kasar ta Najeriya dai ya kai ga haramta mallakin kadarori da ma mukamai na gwamnati, sannan kuma a arewa ya yi sanadiyar zubar da jini da ma asara ta rayuka, ga matsalar dan kasa da bakon da ta dauki lokaci tana taka rawa a siyasa da zamantakewa cikin kasar ta Najeriya.

Karte Nigeria Englisch Deutsch
Hoto: DW

Duk da cewar dai kashi na uku karamin sashe na daya na kundin tsarin mulkin kasar ta Najeriya dai ya ayyana dan kasar a matsayin mutumin da aka haifa bayan 'yancin kai ko kuma iyayensa ke zaman 'yan asalin kasar, dai banbancin al'adu da ma na addini dai na zaman karfe ga batun zamantakewa a tsakannin sassan kasar daban daban.

Wane ne dan kasa a Najeria?

To sai dai kuma daga dukkan alamu tana shirin zama tarihi a cikin kundin tsarin mulkin kasar da 'yan majalisar wakilan kasar suka fara shirin gyarawa a cikin wannan mako da kuma a karkashinsa kowane dan kasar da ya share shekaru har 10 cikin kowane sashe to ya zama dan wannan sashe sannan kuma yana iya samun kowace dama a ciki.

Gyaran kuma dake cikin daya a cikin jeri na gyare gyaren kundin da Najeriya ke fatan ka iya kaiwa ga samun sauyi na cigaba da ma kare rigingimu na siyasa da zamantakewar da suka yi katutu ta ko'ina.

To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba dai daga dukkan alamu ra'ayoyi sun banbanta ko cikin zauren majalisar wakilan kasar da, da ranar wannan Talata ta kadammar da shirin gyara a cikin kundin da kuma ya zuwa karshen wannan mako a ke saka ran kawo karshen yunkurin na kawo gyara cikin kasar.

DW_Nigeria_Integration-online6
Dandalin hadin kai a AbujaHoto: Katrin Gänsler

Hon Bello Kaoje dan majalisar wakilan kasar a Jihar Kebbi kuma a fadarsa "akwai bukatar sauyin da ke iya kara hadin kai da ma tabbatar da 'yancin kowa".

Matakin hada kan 'yan kasa

Kokari na hadin kawunan al'umma ko kuma ci da gumi na 'yan kasa dai, batun na dan kasa da 'ya'yan baki dai na sauyin salo da ma launi a matakai daban daban na hukumomin kasar ta Najeriya.

Ko da ranar wannan Talata dai alal misali zauren majalisar tarrayar da ya fara batun gyaran kundin dai ya kai ga nadin wani kwamiti da nufin nazarin kame wasu 'yan arewacin kasar sama da dari uku tare da lakaya musu take na Boko Haram a jihar Rivers a wani abun da a fadar Abdurahmman Kawu Sumaila dake zaman wani dan majalisa ta wakilan a Kano ke zaman "alamu na yadda bako da dan garin ke yin tasiri ga rayuwa da walwalar al'umma cikin kasar".

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal