1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwiwowi sun yi sanyi a Zimbabuwe

November 16, 2017

Jama'a a Zimbabuwe sun soma nazarin rayuwa a kasar ba tare da kasancewar shugaba Robert Mugabe a matsayin jagora mai mulkin kasar ba.

https://p.dw.com/p/2nijJ
Simbabwe Krise Straßenszenen aus Harare
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Al'umar kasar Zimbabuwe sun soma hasashen yiwuwar ci gabar rayuwa a kasar ba tare da shugaba Robert Mugabe a matsayin jagora mai mulki a kasar ba. A ranar Laraba ne dai shugaba Mugaben ya tabbatar da kasantuwar karkashin daurin talala, bayan karbe iko da dakarun kasar suka yi.

Galibin matasan kasar dai ba su san da wani a matsayin shugaba in banda Mr. Mugabe ba, wanda ke jagorantar kasar tun a shekarar 1980, lokacin da kasar ta sami 'yanci daga Birtaniya.

Tuni kungiyar kasahen Afirka ta AU ta bayyana halin da kasar ke ciki a matsayin juyin mulki a takaice, duk da cewar dakarun da ke rike da ikon sun nesanta manufarsu da hakan. A ranar Alhamis ne kuwa kungiyar hada kan kasashen kudancin Afirka za ta yi zama kan halin da Zimbabuwen ke ciki a kasar Botsawana.