Gwarzo Umaru Aliyu ya kammala aiki | Zamantakewa | DW | 02.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gwarzo Umaru Aliyu ya kammala aiki

Umaru Aliyu ya shafe shekaru 41 ya na aiki a sashen Hausa tun lokacin ofishin wanann tasha yana birnin Kolon har kuma ya dawo nan birnin Bonn

 Kusan a iya cewa duk sashen Hausa na DW babu wanda ya kai Umaru Aliyu dadewa ya na aiki, kuma idan ka dauki dukkan tashar DW da ke watsa shirye-shiryen ta a harsuna fiye da 30, mutum biyu ne zuwa daya suka fishi dadewa.

Mun gutsuro muku kadan daga muryarsa a shekarar 1977 lokacin da suka gabatar da shiri na bikin rufin ginin tashar DW a birnin Kolon shi da marigayi Ado Gwadabe, wato lokacin yana matashi.

Jiya ba yau ba inji masu iya Magana, Malam Thomas Moesch, shugaban sashen hausa na DW wadda ya zo sashen lokacin Umaru Aliyu yana da kusan shekaru 30 a da fara aiki, ya yi bayanin yadda kwazon Umaru Aliyu yake.

Hajiya Murjanatu Katsina wadda a yanzu shekarun ta 90 tana daya daga cikin tsaffin ma´aikata da suka bude Sashen Hausa na DW. Ta yi aikin wani dan takaitaccen lokaci da Malam Umaru Aliyu. A hirar su da Mohammad Abba Katsina, ta ce za ta iya tuna irin yadda suka yi aiki a wancan lokaci cikin raha da annashuwa.

Umaru Aliyu (DW)

Ibrahim Biu shi ma guda ne daga cikin tsaffin ma´aikatan, kana tsohon directar a hukumar zabe ta Najeriya kuma shugaban gidan radiyon Progress FM mai zaman kansa a Gombe ya yi aiki tare da Umaru Aliyu wato baban gayu a cewar sa sunan da suke kiran sa dashi kenan a wancan lokacin.

Idan za a yi maganar ma'aikatan DW da Umaru Aliyu ya dade ya na hulda da su, dole a ambaci Mahaman Kanta wakilinmu na Yamai a Jamhuriyar Nijar, domin sun shafe shekaru suna aiki tare.

Umaru Aliyu ya yi bayanin yadda suka tsinci kansu farkon zuwan sa nan turai, da kuma zayyana wasu daga cikin abokan aiki a wancan lokacin har da irin kalubalen da ya fuskanta tsawon shekaru 41.

Za'a iya sauraron shirin Hantsi na musamman game da Umaru Aliyu daga kasa.

 

Sauti da bidiyo akan labarin