Gwamnatin Togo ta yi tayin sulhu ga ′yan adawa | Labarai | DW | 07.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Togo ta yi tayin sulhu ga 'yan adawa

A daidai lokacin da 'yan adawar Togo ke soma wata zanga-zangar kwanaki uku gwamnatin kasar ta yi masu tayin hawan tebirin sulhu

Gwamnatin kasar Togo ta yi tayin hawa tebirin tattaunawa da illahirin bangarorin siyasar kasar da nufin shawo kan rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar watanni da dama. 

Gwamnatin ta bayyana wannan aniya tata ce a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin a gidan talabijin na kasa, inda ya yi kira ga jam'iyyun siyasa musamman na bangaren adawa kan su nuna dattaku da kuma kishin kasa domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan kasar. 

Wannan kira na gwamnatin kasar ta Togo na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawar kasar ke shirin soma wata zangar-zangar kwanaki uku daga yau Talata domin tilasta wa shugaba Faure Gnassingbe sauka daga mulki, zanga-zangar da kuma ake fargaba rikidewarta zuwa tarzoma kamar yadda ta kasance a watan Oktoban da ya gabata da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 16 da suka hada da sojoji biyu.