Gwamnatin Thailand ta kafa dokar ta ɓaci | Labarai | DW | 21.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Thailand ta kafa dokar ta ɓaci

Hukumomin sun kafa dokar ta ɓaci ne a birnin Bangkok da yankunan da ke kewaye da birnin.

Gwamnatin ta yi haka ne a wani yunƙurin na fuskantar zanga- zangar 'yan adawar ƙasar da ke buƙatar shugabar gwamnatin Yingluck Shinawatra da ta sauka daga muƙaminta tun watanni biyu da suka wuce.

A wani taron manema labrai da ya yi, mataimakin firaministan ƙasar ya ce sun ɗau doka ce ta kwanaki 60 wacce za ta fara aiki daga ranar Laraba saboda halin da ake ciki a ƙasar. Yanzu haka dubban magoya bayan 'yan adawar sun datse wasu titunan birnin Bangkok da shingaye inda harkokin kasuwanci suka tsaya cik.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh