Gwamnatin Sudan tace kofa bude take ga yan gudun hijirarta dake Masar | Labarai | DW | 30.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Sudan tace kofa bude take ga yan gudun hijirarta dake Masar

Kasar Sudan ta bukaci yan gudun hijirarta da suke birnin Alqahira da su koma gida,bayan zanga zanga na yau da yayi sanadiyar mutuwar wasu yan gudun hijirar su 10,a lokacinda dubban yan sanda suka tilasta kawntar da zanga zangar watanni uku da yan gudun hijirar suke yi a wajen ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya dake birni Alqahira.

Karamin ministan harkokin wajen Sudan Ali Ahmed Kerti,yace kofa a bude take ga yan gudun hijirar su koma gida,maimakon halin da suke ciki a yanzu.

Kerti yana a birnin Alqahira a yau din alokacinda yan sandan suka yi anfani da albarusan ruwa da kulaken karfe wajen korar masu tarzomar,yace yanzu an samu canji a Sudan musamman hannu da aka sanya akan yarjejeniyar zaman lafiya,yace basu da dalilin neman mafakar siyasa

Su dai wadannan yan gudun hijira suna neman hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sake duba bukatunsu da tayi watsi da su na sake tsugunad da su a musamman kasashen Amurka,Canada da Australia.

Yanzu haka kuma jamian tsaro na masar sunce mutane 20 ne suka rasa rayukansu a hargitsin na yau