Gwamnatin Sudan ta amince hawa tebrin shawara da yan tawayen Darfur | Labarai | DW | 09.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Sudan ta amince hawa tebrin shawara da yan tawayen Darfur

Gwamnatin ƙasar Sudan, ta bayana amincewa, komawa tebrin shawara, tare da rukunin ƙungiyoyin yan tawayen NRF na yankin Darfur, da su ka yi wasti da yarjejeniyar da a ka cimma da gwamnati, a tantanawar Abujan Nigeria.

Sanarwar da gwamnati ta bayyana yammacin jiya, ta yi nuni da cewar, za a gudanar da shawarwarin tare da mutunta yarjejeniyar da aka cimma, da sauran ƙungiyoyin tawaye, a Tarayya Nigeria.

A wani labarin kuma, hukumomin Khartum, sunyi watsi da zargin da gwamnatin Jamhuriya Afrika ta tsakiya, ta yi masu, na hadasa rikicin tawaye, a wannan ƙasa.

A cewar kakakin gwamnatin Sudan Nafie Ali, shugaba Francois Bouzize, ya ƙago wannan zargi, tare da shugaban Tchad, Idriss Deby, da zumar shafa ma Sudan Kashin kaji.

Suma hukumomin Sudan sun maida buda, ta hanyar tuhumar Tchad, da Jamhuriya Afrika ta tsakiya, da tallafawa yan tawayen yankin Darfur.