Gwamnatin riƙwan ƙwaryar Cote d´Ivoire ta yi murabus | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin riƙwan ƙwaryar Cote d´Ivoire ta yi murabus

Praministan riƙwan ƙwaryar Cote d´Ivoire Charles, Konnan Bany, ya gabatar da murabis ɗin gwamnatin sa, ga shugaban ƙasa Lauran Bagbo.

Wannan murabis, ya biwo bayan wata badaƙala, a game da ɗimbin shara mai guba, da wani kampani ya zubda a Abidjan babban birnin ƙasar, wanda kuma ya zuwa yanzu, ta hadasa mutuwar mutane 3, da galabaita a ƙalla mutane dubu ɗaya da rabi.

A jawabin da yayi ,ta kafofin sadarwa na ƙasa, Charles Konnan Banny, ya ce wannan murabus ya zama wajibi, a matsayin martani na mayuwacin halin da al´ammarin ya jawo a birnin Abidjan.

Shugaba Lauran Bagbo, ya umurci Praminstan, ya sake naɗa sabuwar gwamnati, tun yau alhamis, wadda za ta duƙufa cikin gaggawa a kan binciken masu alhakin wannan ɗayan aiki.

Hukumomin Cote d´Ivoire, sun bukaci agaji daga ƙasashen dunia, domin kawo ƙarshen bila´in guɓacewar iska, da wannan shara mai guba ta hadasa.

Tunni, ƙasar France, ta amsa kiran, tare da tura tawagar ƙurraru.

Rahotani daga Abidjan,sun ce, wasu mazauna birnin sun fara ƙaurace masa.