Gwamnatin Najeriya ta yi sabon yunƙuri wajen tabbatar da tsaro ta hanyar biyan diyya | Siyasa | DW | 26.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gwamnatin Najeriya ta yi sabon yunƙuri wajen tabbatar da tsaro ta hanyar biyan diyya

A karon farko, gwamnatin Najeriya ta fidda maƙudan kuɗaɗen biyan diyya ga waɗanda rikicin bayan zaɓe a 2011 ya shafa bisa tanadin rahoton kwamitin Sheikh Ahmed Lemu

Bildausschnitt von Jonathan Goodluck. French Prime Minister Francois Fillon, left, stands with Nigerian d Vice President Goodluck Jonathan as he meets for talks with leaders of Africa's most populous nation, at the Presidential Villa in Abuja, Nigeria Friday, May 22, 2009. Fillon later told reporters that France was Nigeria's second-largest investor after the United States, and he praised Nigeria for contributing to peacekeeping missions across Africa. (AP Photo/Abayomi Adeshida)

Jonathan Goodluck

A wani abun dake zaman kama hanyar kawo sauyi a cikin matsalar mantawa da rahotannin kwamitocin riginigmun daban - daban a Tarrayar Najeriya, gwamantin ƙasar ta fara aiwatar da rahoton kwamitin Sheikh Ahmed Lemu da ya binciki tashe-tashen hankluan zabe na shekara ta 2011

An dai zubar da jini a Plateau an kuma tashi hankali a Kaduna da sauran sassa na Arewaci da ma ɗaukacin Tarrayar nigeria a wani abun da ya mamaye sake dawowar demokaradiyar kasar ta Nijeriya shekaru 14 da suka gabata.

To sai dai kuma ƙoƙari da ma alƙawari na kawo ƙarshen matsalolin tashe-tashen hankali dai sun ci tura sakamakon gazawar gwamantin ƙasar na aiwatar da jerin rahotannin kwamitocin data nada domin binciken musabbabin rikicin.

Dalilin aiwatar da shawarwarin Kwamitin Sheikh Ahmed Lemu

Da ƙyar da gumin goshi ne dai aka kai ga shawo wasu 'ya'yan sabon kwamitin kawo karshen matsalar rashin tsaron Arewa da fadar gwamantin ƙasar ta kafa a cikin wannan mako suka kai ga amincewar taka rawa bayan korafin su na bata lokaci ba tare da gwamantin aiwatar da nata bangaren ba.

Matsayin kuma da daga dukkan alamu ya tilasta gwamntin sauyin rawa tare da aiyyana aniyar ta, ta fara aiwatar da rahoton kwamitin Sheikh Ahmed Lemu daya nemi biyan diyya ga wadanda rikicin zaɓen ƙasar na shekara ta 2011 ya rutsa dasu.

Ya zuwa yanzu dai gwamantin ta sanar da diyyar Naira Miliyan Dubu Biyar da Bari Bakwai da Hamsin da tace za'a raba su cikin wasu jihohi tara na arewacin kasar da rikicin yayi kamari.

Wata sanarwar fadar gwamantin kasar ta Aso Rock dai ta ce Jihar Katsina ce zata samu kaso mafi tsoka da alumarta suka samu Naira Miliyan Dubu daya da Miliyan Dubu Dari Tara, sai kuma Bauchi da zata samu Miliyan dubu Daya da miliyan dari biyar domin biyan diyyar nata yayan da rikicin ya kai ga yin ta'adi kansu.

Kanon dabo dai zata samu Naira Miliyan 994 jihar Adamawa 420, a yayin kuma da jihar akwa Ibom zata samu naira Miliyan 43.

Yadda ake fassara sabon yunƙurin gwamnati

Ana dai kallon sabon yunkurin a matsayin alamu na farkawa daga baccin da ya dauki tarrayar Nijeriya ya kaita ga fuskanatar kalubale mafi girma tun bayan yakin basasar kasar shekaru 40 din da suka gabata.

To sai dai kuma a cewar Kakakin fadar Dr Reuben Abati ya ce gwamantin ta daɗe idonta biyu kuma tana lura da duk abun dake faruwa a ko'ina a ƙasar.

Wannan gwamantin kun sani bamu taba kyale wani abun da zaka kira keta doka ba. Don mun biya diya ba yana nufin mun kyale aiyyukan laifi ba ko na zabe koma wane iri.

Kar ku manta tashin hankali ko na zabe koma wane iri babban laifi ne haka kuma dokokin kasar mu dama dokokin zabe suka tanadar. Gwamanti na aiki ne kawai cikin tsarin da ke kunshi a rahoton kwamitin sheik Lemu.

Zargin mahukuntan Najeriya da siyasa da rayukan al'umma

Kauda ido ga laifukan ƙasar ta Najeriya ko kuma siyasa da rayukan al'umma dai a baya an zargi mahukuntan na Abuja da nuna son kai da siyasa a cikin rikicin da a mafi yawan lokuta kan ambato manyan masu uwa a gindin murhu da hannu a cikin hura wutarsa.

To sai dai kuma sabon matakin na zaman alamun sauyi ga Abujar dake tunkarar ƙalubale mafi girma da kuma ke bukatar goyon baya da fahimtar talakawan ƙasar bisa matakan da take dauka kan rigingimun tsaron kasar.

Murtala Hamman Yaro Nyako dai na zaman gwamnan jihar Adamawa kuma daya daga cikin gwamanonin da jiharsa ke fama da rigingimu a arewan kuma a ceewar sa matakin na Abuja na zaman alamu na kama hanyar sauya tunani

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabbabin matakan na Abuja ga kokarin ganin ƙarshen tashe tashen hankulan da sake tabbatar da ɗora kasar bisa turba ta cigaba.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin