1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Masar ta cire dokar ta baci

November 12, 2013

Mahukutan kasar Masar sun ce za su mutunta hukuncin kotu kan kawo karshen aiki da dokar ta baci.

https://p.dw.com/p/1AG8q
Hoto: DW/A. Wael

Gwamnatin wucin gadin kasar Masar ta kawar da dokar ta baci da ake aiki da ita na tsawon watanni uku da suka gabata.

Majalisar gudanarwar kasar ta ce dage dokar ta bacin da dokar hana yawan dare na da nasaba da mutunta hukuncin wata kotu, da ta ce dokar ta kawo karshe. Ranar Alhamis mai zuwa dama dokar ke kawo karshe.

Ranar 14 ga watan Agusta Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Masar Adly Mansour ya kafa dokar ta bacin, sakamakon zanga-zangar da ta biyo bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Mursi da sojoji suka yi, kana a cikin watan Satumba gwamnati ta ayyana tsawaita dokar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba