Gwamnatin Kwango za ta saki ′yan adawa | Labarai | DW | 20.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Kwango za ta saki 'yan adawa

A wani mataki na zuba ruwa a wutar rikicin siyasar kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, gwamnatin kasar ta sanar da sakin 'yan adawa guda 24 daga gidan kaso.

Joseph Kabila Kabange

Shugaban kasar Kwango Joseph Kabila Kabange

Gwamnatin kuma ta amince da bude wasu gidajen talbijin guda biyu mallakar 'yan adawa. Hakan dai na zuwa ne kafin zabe mai zuwa na shugaban kasa a kasar ta Kwango. Sai dai tuni dama 'yan adawar ke zargin Shugaba Joseph Kabila, da ke mulki tun bayan rasuwar mahaifinsa Laurent- Desire Kabila a shekara ta 2001, da neman makalewa kan karagar mulkin kasar, ganin yadda gwamnatin take ikirarin cewa bata da isheshen kudin shirya zaben a wannan shekara.

A baya dai kotun tsarin mulkin kasar ta Kwango ta bai wa shugaba Kabila izinin iya ci gaba da mulki muddin dai ba a samu shirya zabe ba. Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango dai ba ta samu sauyin gwamnati ba wanda aka yi shi cikin ruwan sanhi tun bayan da ta samu mulkin kai a shekara ta 1960.