Gwamnatin jihar Adamawa a Najeriya ta bukaci karin dakaru | Labarai | DW | 07.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin jihar Adamawa a Najeriya ta bukaci karin dakaru

Bukatar wannan jiha da ke arewa maso gabashin Najeriya na zuwa ne bayan da dakarun Kungiyar Boko Haram suka kwace wasu garuruwan jihar.

Gwamnan jihar Bala Ngilari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga taron manema labari a Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

A cewar gwamna Ngilari neman karin dakarun tsaron ya zama dole duba da yadda lamura ke kara tabarbarewa a yankin na arewa maso gabashin kasar .

Idan dai ba a mantaba, gwamnatin Najeriyar ta sanya dokar tabaci a jihohin Yobe da Borno da Adamawa a watan Mayun shekarar bara, inda ita jihar ta Adamawa, da yawa mutane ke gani an sanya mata dokar ne saboda kare fadadar ayyukan masu tada kayar bayan.