1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rikicin siyasa ya jefa gwamnatin Italiya a rudani

Suleiman Babayo AH
January 18, 2021

Firamnista Giuseppe Conte na kasar Italiya da gwamnatinsa sun shiga tsaka mai wuya sakamakon sabon rikicin siyasa da ya janyo gwamnati rasa rinjaye da take da shi a majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/3o52A
Italien Premierminister Giuseppe Conte im Parlament
Hoto: Alessandra Tarantino/REUTERS

Firamnista Giuseppe Conte na Italiya ya gwagwarmaya bisa iya kare karyewar gwamnatinsa sakamakon rasa goyon baya a karamar majalisar dokoki, bisa matakin sake kaddamar da tattalin arziki bayan annobar cutar coronavirus.

Conte ya rasa karamin rinjaye da yake da shi lokacin da wani minista ya koma bangaren tsohon firaminista Matteo Renzi. Shi dai Renzi yana shan suka saboda yadda ya nuna neman samun mulki lokacin da kasar ke tsaka da annobar cutar coronavirus. A wannan Litinin Firamnista Giuseppe Conte yake gabatar da jawabin ga majalisar wakilai sannan kuma gobe Talata ga dattawa. Komai ka iya faruwa daga bisani saboda rasa rinjaye da gwamnatin ta Italiya ta yi a cikin majalisar dokoki.