Gwamnatin hadaka ta zamo dole a Turkiya | Labarai | DW | 08.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin hadaka ta zamo dole a Turkiya

Sai dai akwai yiwuwar a samu cikas wajan kafa gwamnatin hadakar ganin irin yanda 'yan adawa ke dari darin yin kawance da jam'iyyar ta AKP

A kasar Turkiya Jam'iyyar AKP ta shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan na shirye shieyen soma zama tebirin tattaunawa da jami'iyyun adawar kasar domin kafa sabuwar gwamnatin hadaka biyon bayan kayin da ta sha a zaben 'yan majalissar dokokin da ya wakana a kasar a karshen makon jiya.

Wannan dai shi ne karo na farko tun bayan kafata yau shekaru 13 da jami'iyyar AKP za ta kasa samun sukunin gudanar da milki ita kadai. Sai dai masu lura da al'amurran siyasar kasar ta Turkiyya na ganin ba karamin jan aiki ba ne ke a gaban jam'iyyar ta AKP ganin irin yanda jam'iyyun adawa da dama ke dari darin kulla kawancan da ita.

Wasu na ganin akwai yiwuwar a sake komawa wani sabon zaben idan har aka samu cikas wajan kafa sabuwar gwamnatin ta hadaka.Sakamakon wanann zabe dai ya saka kasar ta Turkiya a cikin wani hali na rashin tabbas inda tuni darajar kudin kasar na Lire ta fadi warwas.