Gwamnatin farar hula a Burkina Faso | Labarai | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin farar hula a Burkina Faso

Shugaban rikon kwarya na Burkina Faso Kanar Isaac Yacouba Zida, na ci gaba da ganawa da bangarori daban-daban na kasar domin kafa sabuwar gwamnatin farar hula.

A safiyar wannan Litinin din ce dai (03.11.2014) shugaban ya gana da jakadun kasashen waje da ke birnin na Ouagadougou, inda yayin wannan ganawa. Kanar Isaac Zida ya tabbatar da aniyarsa ta amincewa da kafa gwamnatin farar hula da zata jagoranci rikon kwaryar kasar, inda ya ce za'a girka gwamnatin ce dai dai da yadda tsarin mulki ya tanada. Sai dai kundin tsarin mulkin kasar ta Burkina Faso da sojojin suka ce sun soke, ya ce idan har babu shugaban kasar, to shugaban majalisar dokoki ne zai rike mukamin har ya zuwa zabe. Daga nashi bangare, kwamitin zaman lafiya na Tarayyar Afirka zai yi zaman taron a birnin Addis Ababa kan batun kasar ta Burkina Faso, karamar kasa da ke yankin Sahel mai kunshe da al'umma akalla miliyan 17, inda al'umma ta fara komawa ga harkokin ta na yau da kullum.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu