Gwamnatin Bulgariya ta yi murabus | Labarai | DW | 20.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Bulgariya ta yi murabus

A wani zama da majilisar dokokin Bulgariya ta yi a Sofia babban birnin kasar, firaministan kasar, Boyko Borissov ya sanar da yin murabus na gwamnatinsa.

Da ranar nan ne kuma a hukumance za a mika wannan bukata a zaman karshe na majalisar ministoci. An dau wannan mataki ne biyo bayan wata gagarumar zanga-zmga da aka gudanar domin nuna adawa da matakan tsuke bakin aljihu da kuma kara kudin wutar lantarki.Dubun dubatan 'yan zanga-zanga da suka hada da 'yan adawa a majalisar dokokin kasar ne suka gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadin da ta gabata suna masu kira ga gwamnati da ta yi murabus. A daura da wannan zanga-zangar ne kuma wani matashi ya cunna wa kansa wuta a birnin Varna da ke gabashin kasar. A dai halin yanzu yana kwance asibiti inda yake karbar maganin sakamakon mummunar kunar da ya samu .

A watan Yulin shekarar 2009 ne dai Borissov ya karbi ragamar mulki. Da a watan Yuli ne kuma za a gudanar da zaben majalisar dokoki . To amma yanzu an matso da gudanar da zaben a watan Afrilu. Ita dai kasar ta Bulgariya na zaman kasa mafi talauci tsakanin kasashen kungiyar Tarayyar Turai.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal

I