1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji manyan matsaloli

Ubale Musa M. Ahiwa
May 31, 2023

Sabuwar gwamnatin Najeriya da ta yi alkawarin sauya da dama cikin kasar, ta fara mulki tare da gadon jiga-jigai na ayyukan da ke iya lashe daukacin kudin kasar.

https://p.dw.com/p/4S1z3
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Bayan share lokaci ana biki, sannu a hankali idanun sabawar gwamnatin Najeriya na budewa bisa dimbin rikicin da ke gaban kasar a halin yanzu. Na baya-baya dai na zaman jeri na muhimman ayyukan da ke fuskantar barazanar komawa ayyuka irin na baban giwa a yanzu haka. Kama daga manyan tituna da gadoji ya zuwa batun samar da wutar lantarki ko bayan bututun iskar gas dai, tsohuwar gwamnatin kasar dai ta sa kafa ta bar mulkin Najeriyar da muhimman ayyukan da ta fara amma kuma rashin kudi da lokaci ya sa ta barin su.

Tituna irin na Kano zuwa ga Abuja da dan uwansa na Badun ya zuwa birnin Ikko, ko bayan bututun iskar gas din da ya hade Ajakuta zuwa Kano da ma hanyar da ta hade Bodo zuwa Bonny a yankin Neja Delta, ko bayan layin dogo na Ibadan zuwa Kano dai, muhimman ayyuka 33 ne da aka kiyasta sun kai Naira Tiriliyan 16 tsohuwar gwamnatin ta Buhari ta watsar ta wuce a wani abin da ke zaman barazana mai girma a kasar.

Nigeria Einweihung des neuen Präsidenten Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Shugaba Bola Tinubu na a tsakanin dorawa zuwa gaba da mai da hankali ga kammala ayyukan na Buhari, ko kuma mantawa tare da gina dan bar sababbi. Abun kuma da ke iya kai kasar zuwa jeri na ayyukan baban giwar da suka mamaye daukacin kasar a lokaci mai nisa. Tsohuwar al'adar dauri, ko kuma neman hanya ta cigaba dai, Najeriyar ta yi nisa a wajen ayyuka irin na baban giwar da suka cika gari kuma ke zaman tarnaki da ke da girman gaske ga ci gaban kasar.

Har ya zuwa yanzu dai alal ga misali, Abujar na neman mafita bisa takaddamar kamfanin karafa na Ajakuta da ke zaman irin sa mafi girma da kuma ya share shekaru 40 da doriya yana zaman jiran a kammala. Nakasu cikin harkar mulki, ko kuma neman hanya ta ci gaba dai an dauki lokaci ana zargin ‘yan mulkin kasar da ba da ayyuka tare da karbar na goro ba tare da kaiwa ya zuwa tabbatar da kammala su domin amfani na 'yan kasa ba.

Ayyukan Tiriliyoyin Nairori ne dai alal ga misli gwamnatin kasar ta ba da kwangilar su a makonnin karshen mulkin cikin kasar da ke ta korafin rashin kudi. To sai dai kuma a fadar Sulaiman Adamu da ke zaman tsohon ministan ruwan kasar, gwamnati na zaman karbi in karba cikin kasar da ke fuskantar babu.