Gwamnatin Birtaniya ta samu izinin ficewa daga EU | Labarai | DW | 09.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Birtaniya ta samu izinin ficewa daga EU

'Yan majalisar dokokin kasar Birtaniya sun bai wa Firaminista Theresa May damar soma ayyukan ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai.

UK | Britisches Unterhaus bestätigt Brexit (picture-alliance/empics)

Majalisar dokokin Britaniya yayin karanta sakamakon zaben da ya bada izinin fice wa daga EU

Da babban rinjaye ne dai 'yan majalisar dokokin kasar Birtaniya suka amince da wannan mataki, kamar yadda sakamakon ya nunar inda 'yan majalisa 494 suka kada kuri'ar amincewa, yayin da 122 suka nuna adawarsu da hakan bayan da aka shafe kwanaki da dama ana fafata mahawara kan wani kundi mai shafuka 140 da ya kunshi wannan batu.

Wannan kundi da ya samu amincewa ta farko kuma mai babban muhimmanci, zai bai wa Firaminista Theresa May damar amfani da kudiri na 50 na yarjejeniyar Lisbon da ke bada damar kaddamar da tattaunawa ta ficewar kasar ga baki daya daga kungiyar ta Tarayyar Turai cikin shekaru biyu masu zuwa.