1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Rasha

Mohammad Nasiru Awal AS
March 14, 2018

Jami'an diplomasiyyar Rasha su 23 gwamnatin London ta kora dangane da takaddamar harin guba kan wani tsohon dan leken asirin Rasha.

https://p.dw.com/p/2uKwu
Großbritannien Theresa May, Premierministerin
Hoto: Reuters/Parliament TV

A matsayin martani dangane da harin sinadari mai guba a yankin Salisbury da ake zargin Rasha da kai wa wani tsohon jami'in leken asirinta, gwamnatin Birtaniya ta kori jami'an diplomasiyyar Rasha su 23 daga kasar. Bugu da karin gwamnatin ta Birtaniya karkashin jagorancin Firaminista Theresa May ta ce ba za ta tura wakilan gwamnati da na gidan sarauta zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da Rasha za ta dauki nauyinshi nan da wasu watanni masu zuwa ba.

A lokacin da take magana gaban majalisar dokoki a birnin London May cewa ta yi.

"Za mu dakatar da dukkan huldodi na tuntubar juna tsakanin manyan jami'an Birtaniya da Rasha, ciki har da janye goron gayyatar da muka ba wa ministan harkokin waje Lavrov na ziyartar Birtaniya. Muna kuma tabbatar da cewa ba bu wani minista ko wani dan gidan sarautar Ingila da zai halarci gasar cin kofin duniya na lokacin bazara a Rasha."

Birtaniya dai na zargin Rasha da amfani da guba kan tsohon jami'in leken asirinta Sergey Skripal da 'yarsa a Birtaniya, inda kuma ta nemi Rasha ta yi bayani, amma Rasha ta ce ba ta samu wata bukatar yin haka a hukumance ba.