Gwamnatin Afirka ta Kudu za ta yi amfani da sojoji wajen dakile hare-hare kan ′yan Afirka | Labarai | DW | 21.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Afirka ta Kudu za ta yi amfani da sojoji wajen dakile hare-hare kan 'yan Afirka

Gwamnatin Afirka ta Kudu za ta yi amfani da sojoji wajen dakile hare-hare kan 'yan Afirka

Kasar Afirka ta Kudu ta bayyana shirin fitowa da sojoji domin tabbatar da doka da oda cikin yankunan birnin Johannesburg da ake samun tashe-tashen hankula nuna kyamar bakin 'yan kasashen ketere.

Minsitar tsaron kasar Nosiviwe Mapisa-Nqakula ta tabbatar da haka a wannan Talata, inda take cewa amfani da sojoji ya zama tilas inda haka ke zama matakin karshe mayar da zaman lafiya da dakile masu aikata laifuka. Akwai baki daga sauran kasashen Afirka da suke tserewa daga kasar ta Afirka ta Kudu, domin tsira da rayukansu, sakamakon hare-hare da suke fuskanta.