1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na zanga-zanga a Senegal

Suleiman Babayo AH
March 23, 2023

Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya jaddada daukan matakan tabbatar da zaman lafiya bayan zanga-zanga sakamakon ci gaba da gurfanar da jagoran 'yan adawa a gaban kotu.

https://p.dw.com/p/4P9Ec
ECOWAS I Senegal I Shugaba Macky Sall
Shugaba Macky Sall na kasar Senegal Hoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya dace na matakan tabbatar da doka da oda a kasar, yayin da ake ci gaba da samun zanga-zangar kan shair'ar da ake yi wa jagoran 'yan adawa na kasar Ousmane Sonko, lamarin da ya janyo mutuwar mutum daya.

An dai samu tashe-tashen hankula a birane da dama kan shair'ar da ake yi wa Sonko kan zargin bata suna, abin da ake ganin zai shafi takarar da jagoran 'yan adawa ke shirin yi a zaben shekara mai zuwa ta shekara ta 2024. Ana zargin dan dawan da kalaman bata suna ga ministan a gwamnatin kasar.

Ita dai Senegal tana cikin kasashe masu kwanciyar hankali na siyasa a yankin yammacin Afirka.