Gwamnan Aden ya tsallake rijiya da baya | Labarai | DW | 15.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnan Aden ya tsallake rijiya da baya

Aidarus al-Zubaidi wanda babban jami'in gwamnatin Yemen ne ya tsira da ransa ba tare da samun ko da gwarzane ba daga wani harin kunar bakin wake a birnin Aden.

Gwamnan Aden da ke Kudancin Yemen ya tsallake rijaye da baya a wannan Jumma'ar (15.07.2016), a wani harin kunar bakin wake da jami'an tsaro suka zargi kungiyar al-Qa'ida da kaddamarwa. Sai dai kuma uku daga mutanen da ke rufa masa baya sun sami raunuka lokacin da wata mota cike da bama-bamai ta durfafi ayarin motocin da ke cikin tawagar gwamna Aidarus al-Zubaidi.

Manyan jami'an gwamnatin Yemen da hafsoshin soje sun saba fuskantar hare-hare tun bayan da Aden ya zama babban birnin kasar na wucin gadi sakamakon rikicin da ake fama da shi a Sana'a. Ko da a watan Disemba na bara sai da Jaafar Saad tsohon gwamnatin lardin ya rasa ransa ta wannan hanya.

Tun watan Maris na 2015 ne dai dakarun gwamnati Yemen bisa tallafi Saudiyya da kawayenta ke baiwa hamata iska da 'yan tawayen Huthi wadanda ke samun goyon bayan Iran da nufin kakkange madafan iko. Ya zuwa yanzu dai wannan rikici ya lamshe rayukan 'yan Yemen dubu shida da 400.