Gwagwarmayar Willy Brandt ta yaki da mulkin kama karya | Zamantakewa | DW | 18.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gwagwarmayar Willy Brandt ta yaki da mulkin kama karya

A wannan Larabar ce (18.12.2013) Willy Brandt ya cika shekaru 100 da haihuwa. Brandt ya yi gwagwarmaya da Hitler da masu neman karfafa mulkin kama karya a Turai.

A ranar bakwai ga watan Disamba na shekara ta 1970 Willy Brandt ya kama hanyar zuwa ziyara a Poland, tare da burin sanya hannu kan yarjejeniyar hana amfani da karfi kan juna da amincewa iyakokin kasashen juna da aka zana bayan kare yakin duniya na biyu. Wannan ziyara dai bata zama mai sauki ba, bisa lura da rashin imanin da 'yan Nazi suka aikatawa al'ummar kasar ta Poland a lokacin yakin, musamman kakkafa sansanonin gwale-gwale da kisan miliyoyin al'umma a kasar.

Babban abin da ya dauki hankali a lokacin wannan ziyara kuma abin da ya shiga kundin tarihi a duniya baki daya shi ne durkusawar da Brandt ya yi a wani dandali na tunawa a Warsaw, abin da ya zama alamar neman gafarar Jamus daga al'umar kasar ta Poland. Hakan ya nuna cewar Brandt wanda a duk tsawon rayuwarsa ya yi gagwarmaya da mulkin Hitler, ya dauki nauyi amma ba alhakin abubuwan da suka faru a zamanin mulkin na Hitler ba kamar yaddda Alfred Grosser ke cewa.

Willy Brandt im Wahlkampf 1969

Lokacin da Willy Brandt ke yakin neman zabe a 1969

Ya ce "ko da shi ke bashi da laifi, kuma ba shi ne ya aikata abubuwan da suka faru ba, amma shugaban gwamnatin na Jamus ya dauki nauyi a kansa na abubuwan da suka gudana a tarihi, ya kuma dauki alhakin wannan nauyi a kansa."

A nan Jamus da kuma a Poland, an sami wadanda suka soki Willy Brandt saboda wannan kaskantar da kansa da ya yi, to amma ga mutane da yawa wannan mataki da ya dauka ba wani abu bane illa nunar da cewar babu abin da ke gabanta illa neman zaman lafiya. Shekara guda bayan wannan ziyarar ta Poland aka bawa Willy Brandt lambar zaman lafiya ta Nobel.

Shi dai Willy Brandt an haife shi ne ranar 18 ga watan Disamba na shekara ta 1918, tare da amsa sunan Herbert Karl Frahm a garin Lübck. Tun ya na karaminsa, kakansa ya kusantar dashi ga jam'iyar SPD kuma daga baya ya shiga bangaren jam'iyar ta masu matsanancin ra'ayi, wadda aka haramta aiyukanta jim kadan bayan da Hitler ya kwace mulki a shekara ta 1933. Karkashin sunan Willy Brandt, ya sami nasarar tserewa zuwa Norway, inda daga can ya shiga gwagwarmaya ba ma da mulkin Hitler kadai ba amma har da duk masu neman karfafa salon mulkin kama karya a Turai.

Brandt ya dawo nan Jamus a shekara ta 1947, inda Franz Josef Strauss ya zarge shi da kasancewa mai cin amanar kasa tare da tambayrsa shin me ya yi a tsawon shekaru 12 a ketare, me kuma ya dawo yi yanzu a Jamus.

Duk da adawar da ya yi ta fuskanta, amma Willy Brandt ya sami nasarar kasancewa magajin garin Berlin a shekara ta 1957, sa'annan a shekara ta 1969 aka zabe shi a matsayin shugaban gwamnatin Jamus. Daga cikin al'amuran da suka faru, wadanda bai ji dadinsu ba, har da gina katangar Berlin a shekara ta 1961. A daya hannun daga cikin al'amuran da ya sami nasarorinsu, har da kusantar da kasashen gabaci da na yammacin Turai da kuma kusantar da kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaban masana'antu.

Bilder zu Willy Brandt und Polen

Ziyarar Willy Brandt kasar Poland bayan ya zama shugaban gwamnatin Jamus

Daya daga cikin abokan tafiarsa a dandalin siyasa, wato Shridat Ramphal ya ce Willy Brandt dai mutum ne da a zamanin rayuwarsa ake iya cewa duniya gaba daya ita ce kasarsa.

Ya ce "Brandt mutum ne da babu ruwansa da kinshin kasa, babu ruwansa da kyamar wani jinsi, babu ruwansa da kyamar wani addini. Shi mutum ne da ake iya cewa duniya gaba daya ita ce kasarsa. A ra'ayi na, ya yi imanin cewar kasarsa ita ce duniya baki daya, kuma aikin dake gabansa a wannan matsayi shi ne tabbatar da ganin cewar ta zama wuri mai kyau, mai albarka."

Brandt ya zama mutumin da ke da farin jini, wanda aka yi alfahari da shi tun daga nahiyar Afrika har ya zuwa Turai da sauran yankunan duniya. Daya daga cikin aiyukan da ya yi a zamanin rayuwarsa, shi ne kirkiro hukumar hadin kai tsakanin kasashen arewa da na kudu, wato tsakanin kasashe masu ci gaban masana'antu da kasashe masu tasowa bisa manufar kyautata zamantakewa tsakaninsu.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Ahmed Salisu