Gwagwarmayar Museveni na Yuganda | Zamantakewa | DW | 26.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gwagwarmayar Museveni na Yuganda

Takaddama a kan dokar haramta auren jinsi a Yuganda, ya sanya duniya mayar da hankali kan hakikanin rayuwar da gwagwarmayar shugaba Yoweri Museveni.

Bayan kwan gaba kwan baya dangane da dokar haramta yin luwadi da madigo a Uganda, a karshe dai shugaba Yoweri Musaveni ya rattaba hannu tare da sanar da hukunci mai tsanani akan duk wanda aka sameshi da laifin aikata luwadi a kasar. Sai dai abin tambaya shi ne dalilan da suka sanya shugaban jan kafa, gabannin sanya hannu akan dokar, wadda kungiyoyin kare hakkin jama'a, da kasashen yammaci da kuma Amurka ke yin suka a kanta.

Tun bayan daya haye karagar shugabanci a shekara ta 1086, Yoweri Museveni ya yi kokarin inganta ci gaban kasar, fiye da gwamnatin da ta gabata. A matsayinshi na mai fafutukar neman 'yanci, ya yi adawa da mulkin kama karya na Idi Amin a shekarun 1970, kana daga baya Milton Obote. Museveni ya sha nuna adawarsa da cin hanci da rashawa, a lokaci guda kuma ya soki shugabannin da kan dare karagar mulki su yi kakagida, tare da jaddada cewar ba zai kasance a akan karagar mulki fiye da wa'adin mulki biyu, kamar yadda kundun tsarin mulki ta tanadar ba.

Wannan ne ya sanya kasar ta kulla abokataka da kasasahen yammaci, ba tare da la'akarin da cewar jam'iyyarsa ta NRM ce kadai take shekae ayarta a wannan kasa dake yankin gabashin Afrika ba. To sai dai Yugandan ta samu bunkasar tattalin arziki a karkashin mulkin Museveni, musamman lokacin wa'adin mulkin mulkinsa na biyu, inda aka samu bunkasar tattalin arziki daga kashi biyar zuwa 10 daga cikin100. Kazalika rayuwar talauci ya ragu a kasar. Kasanvcewar a shekarun 1990 sama da rabin al'ummar kasar ne ke rayuwa cikin kangin talauci na kasa da dala guda a ko wace rana, amma a shekarun 2005 yawansu bai shige kashi 31 daga cikin 100 ba.

Ha'ila yau a al'ummar Yugandan na yi wa Museveni kallon gwarzo a bangaren inganta harkokin rayuwa dama fannin kula da lafiya. Kamar yadda wannan 'yar kasar ta nunar;

" Ni ina goyon bayan mai girma Museveni, kasancewar tun da aka haifeni shine yake mulki, kuma na cewar kafin ya hau shugabanci ana gwabza yaki".

Museveni ya kasance zakaran gwajin dafi tsakanin sauran kasashen Afrika wajen yaki da cutar Aids da ke haddasa asarar rayukaa nahiyar. Wannan mataki na kampaign ya samu nasara, domin a shekarata 2004 MDD ta ce kashi shida na yawan al'ummar ne suke dauke da kwayar cutar HIV, idan aka kwatanta da kashi 18 na shekarar da ta gabata.

Ya ce "Tun daga shekara ta 1971 nake fafutuka. Neman 'yancin kan 'yan Uganda ya dauki shekaru 16. So ake yanzu in yi watsi da wannan tafiya a tsakar hanya? Siyasar ita kanta fafuka ce.Banbancin kawai shine yanzu muna fafuka ne cikin gwamnati amma ba daga daji ba".

An haifi Yoweri Museveni a ranar 15 ga watan Augusta na shekara ta 1944 a yankin kudu maso yammacin kasar da ta kasance a karkashin mulkin mallaka na Britaniya. Ya yi karatunsa a bangaren tattalin arziki a da kimiyyar siyasa a jami'ar Darussalam a makwabciyar watau Tanzaniya, inda daga baya yayi gudun hijira. Ya sake tafiya gudun hijira a shekara ta 1971, bayan da Idi Amin ya kifar da mulki. Museveni da sauran 'yan Yugandan da suka yi gudun hijira sun hade da sojojin Tanzaniya a shekarata 1978, cikin su har da Milton Obote, wanda ta haka ya sake darewa karagar mulki.

Acewar shugaban adawan Yugandan Kizza Basigye dai " abun takaici ne ganin cewar cikin shekaru 50 na samun 'yancin kai, babu shugaban da ya taba mikawa na gabansa mulki cikin kwanciyar hankali."

Tun daga wannan lokaci ne shugaban na Yuganda ke ta fafutuka, har sai da ya dare karagar mulki a shekara ta 1986. Duk da kasancewarsa a karagar Mulki, Museveni ya cigaba da amfani da karfin soji wajen yakar sojojin tawaye dake fada a rewacin kasar a karkashin Joseph Kony.

Dokar haramta Luwadi da madigo daya zartar dai ya janyo masa suka da kakkausar murya daga kasashen yammaci na Turai da Amurka, tare da kira daya janye takararsa bayan shekaru 28 na mulki, kasancewar tuni jam'iyyarsa ta zabe shi a matsayin dan takarata a 2016.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman