Gwagwarmaya kan Aleppo | Labarai | DW | 04.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwagwarmaya kan Aleppo

Gwamnatin Siriya na kokarin ganin Aleppo ya dawo karkashin jagorancinta amma har yanzu 'yan tawaye na rike da yankin gabashin birnin

Dakarun gwamnatin Siriya sun kara da 'yan tawayen da ke ciki da wajen Aleppo, a kokarin da gwamnatin ke yi na ganin ta rage karfin kungiyar IS musamman a wuraren da take da karfi kamar Aleppo.

Gwamnatin ta kaddamar da sabbin hare-haren ne ranar Juma'a a matsayin wani martani ga sabuwar hadakar kungiyoyi 13 da aka kulla, wadanda suka hada har da wani reshe na kungiyar Al-ka'ida, mai suna Nusra Front, da sauran kungiyoyin tawaye. Wannan hadakar kungiyoyin da suka sanya wa suna Ansar al-Sharia ta ce burin ta shi ne 'yantar da Aleppo, wanda ya kasance cibiyar cinikayya da masana'antu.

Tashe-tashen hankulan kasar dai sun kai ga raba wannan birbi zuwa gida biyu, yankin gabashin da ke karkashin 'yan tawaye da kuma yammacin wanda ke karkashin ikon gwamnati